Wasu malamai a jami’ar Toronto da likitocin asibitin ‘St. Michael’s’da ke Toronto kasar Canada sun bayyana cewa mafi yawan magungunan da ake amfani da su domin kara karfin garkuwan jiki wato ‘Vitamins’ basu da yin abin da ake tunanin sunayi.
Likitocin sun gano haka ne bayan binciken da suka gudanar kan wasu magugunan kara karfin garkuwa kamar su ‘Vitamin A, B1, B2, B3, B6, B9, C, D da E sannan da ‘Carotene,Calcium, Iron,Zinc, Magnesium da Selenium’.
” Binciken da muka gudanar ya nuna mana cewa wadannan magunguna maimakon su kara wa mutum karfin garkuwar jiki sai dai cutar da lafiyar sa suke yi da idan ba a kula ba mutum kan iya rasa ran sa ma.”
” Yawaita amfani da su kan kawo cututtukan shanyewar bangaren jiki,ciwon bugawar zuciya da sauran su.”
A karshe Likitocin sun bayyana cewa za a iya samun sinadarorin kara karfin garkuwan jiki idan ana cin kay itatuwa, kayan kambu da abinci masu kyau.
Likitocin sun yi kira da a guje wa shan ire-iren wadannan magunguna cewa hakan ne kawai mafita.
Discussion about this post