An nada Kyari wakilin Najeriya a kungiyar kasashe masu arzikin man fetur, OPEC

0

An nada babban Manaja na harkar hadahadar danyen mai a kamfanin mai na Kasa NNPC Mele Kyari, a matsayin wakilin Najeriya a kungiyar kasashe masu arzikin man fetur, OPEC.

Wannan sanarwa ta fito ne daga ofishin Manajan hulda da jama’a na kamfanin mai na kasa, Ndu.

Sanarwar ta ce ministan mai na kasa, Ibe Kachikwu ne ya jagoranci tawagar kamfanin mai din na kasa, NNPC, zuwa taron kungiyar inda a nan ne ya sanar da nadin Mele Kyari.

Kachikwu ya bayyana cewa an yi wa Kyari wannan karrama ne ganin dimbin kwarewar sa a harkar hadahadar danyen mai a Najeriya.

Share.

game da Author