Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ta bayyana cewa Najeriya ta biya mutane 14 da suka fallasa inda barayin kudaden gwamnati suke kimshe kudaden, har ladar naira miliyan 439.3.
Minista Adeosun ba ta bayyana sunaye ba, amma dai ta ce akalla ta ce an kwato naira bilyan 14.8, wadanda suka hada da naira bilyan 7.8, dala miliyan 378 da kuma fam na Ingila 27,800.
Ta ce kudaden wadanda aka maida aljihun Hukumar tattara harajin cikin gida, kuma tuni an rabar da kudin tsakanin tarayya, jihohi da kananan hukumomi.
An samu kudaden ne daga kamfanoni daban-daban wadanda suke rika kin biyan kudaden haraji, daga bisani aka rika fallasa su ta hanyar ‘whistleblowers’.