Siyasar Karamar Hukuma ta fara shure-shuren mutuwa a Najeriya, Daga Mustapha Soron dinki

0

Siyasar karamar hukuma itace tushen siyasa a kowacce kasa. Hasali ma,itace kamar matsayin karatun furamare ga dan boko.

Shi yasa duk dan siyasar da bai yita ba, ana iya yi masa gori akan bashi da grassroot background. Duk girman kasa ta fara ne da mazaba sannan karamar hukuma zuwa jiha har mataki na kasa. Kuma a siyasance ana ganin romon dimokaradiya daga talakawan gari ba attajirai ba.

Babu kan-gado a siyasar da ci gaba zai fara daga sama zuwa kasa kamar kashin dankali.

Kada mu manta da cewa, ita fa karamar hukuma an kafata ne don a jawo gwamnati kusa da talakawa. Wannan shine babban dalilin kirkirarta, amma karamar hukuma ta fara bayar da wasiyar mutuwa a siyasar Najeriya musamman inda nafi sani shine Arewa maso yamma.

Tun lokacin da zaben karamar hukuma ya dawo hannun gwaunatin jiha aka samu matsala.Ita kanta INEC,ai wannan ‘yancin ne ya bata kariya amma ai da tuni wasu sun sakata a aljihunsu tana musu aiki.Zaben karamar hukuma ya zama “one party system.” Hujjata shine zaben Kaduna da Kano. Duk da naji INEC ta wanke na Kano.

Siyasar karamar hukuma tarasa jam’iyyar adawa. Abun mamaki jam’iyun adawa sun daina tsayawa takara saboda rashin yadda da hukumar zaben da take gudanar dashi. Talauta karamar hukuma shi ya kara talauta kauyuka a Najeriya. Misali,duk da cin hanci da rashawa da yayi yawa a karamar hukuma amma dai tana kamanta yin abunda aka kafata don shi. Matsalolin talakawa da yawa ana warware musu tunda ganin gwauna yayi musu wahala ballantana shugaban kasa. Amma da mamaki ace jam’iya 31 bata shiga zabe a jihar Kaduna ba. Suma jam’iyun adawar basu kyauta ba. Wannan kashe dimokaradiya ne.

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author