SOKE YARJEJENIYA DA IRAN: Farashin danyen mai ya tashi

0

Farashin danyen man fetur ya tashi lokaci guda a kasuwar duniya, jim kadan bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana soke yarjejeniyar makamin kare-dangi tsakanin Amurka da Iran.

Duk da rokon da kasashen da ke da kusancin dangantaka da Amurka su ka yi masa don kada ya soke yarjejeniyar, Trump ya rufe ido ya soke yarjejeniyar, wadda tuni da dama a duniya ana yi wa Trump din kallon tabka rashin mutunci, rashin rikon amana da kuma halayya irin ta ‘yan ragabza da gidogancin da bai kamata a ce shugaba ne ke yin irin dabi’un ba.

Da yawan masu adawa da Trump a Amurka na ganin tsige shugaban ne kadai zai iya dawo da martabar kasar daga zubar ma ta da kima da Trump ke yi tun bayan hawan sa mulki.

An dai kulla yarjejeniyar ce tsakanin Iran da Amurka, cikin 2015, kuma soke ta din zai kawo kwakkwaran zaman dar-dar a Gabas ta Tsakiya, zai rikirkita farashin danyen man fetur, kuma zai lalata diflomasiyyar yankin.

A yanzu fetur ya kai kowace ganga daya a kan kudi dala 76.52, ya zuwa karfe 6 agogon GMT na jiya Laraba da yamma.

Kasar China, wacce ita ce kasar da ta fi kowace kasa sayen danyen man fetur daga kasar Iran, farashin man ya kai dala 73.20 a kowace ganga daya.

Masu lura da al’amurran yau da kullum na cewa har ila yau, karin darajar farashin danyen man ya na da nasaba da rage sayar da mai da Iran ta yi ga kasashen yankin Asia da Turai a wannan shekara zuwa 2019 da za a shiga.

Iran ta kasance kasar da ta fi sayar da danyen mai ga kasashen duniya, bayan da janye mata takunkumi a cikin 2016, kasancewa ta amince rage sarrafa makamashin nukiliya da ta ke yi.

Bincike ya tabbatar da cewa a cikin watan Afrilu, Iran ta na fitar da danyen mai har ganga milyan 2.6 a kowace rana.

Baya ga Saudiyya da Iraq, babu kasar da ta kai Iran yawan hako danyen mai a duniya.

Soke yarjejeniyar da Amurka ta yi, ya na nufin kenan nan da kwanaki 180, idan ba a hanzarta shiga tasakani ba, to Amurka za ta iya sa wa Iran takunkumi.

Hakan zai iya harzuka Iran, wadda Amurka ke ganin ta zama barazana ga kasar Isra’ila.

Iran dai ta sha bayyana cewa za ta shafe kasar Isra’ila daga doron kasa, saboda irin yadda ta ke shiga-hanci-da-kudindine ga kasashe irin su Lebanon Jordan da kuma tauye hakkin Falasdinawa.

Dalili kenan kasashe irin su Amurka, Tarayyar Turai da Isra’ila ke ganin mallakar makamin kare-dangi ga Iran babbar barazana ce sosai.

A daya bangaren kuma mummunan rashin jituwar da ke tsakanin manyann kasashen musulmai biyu, Saudiyya da Iran, ya na kan gaba wajen tsoron da ake yi wa Iran ta mallaki muggan makamai kamar nukiliya.

Sau da yawa dai Iran na cewa ta na sarrafa nukiliya ne domin samar da makamashi, ba makamai ba.

Sai dai kuma Amurka, Isra’ila, Turai da Saudiyya duk su na yi wa Iran kallon ta rigaya ta kawo karfi, batun grime mata da aka yi kuwa, duk ya zama tatsuniya kenan.

Musamman kuma ga shi Hausawa na cewa, “Dutsen da ke hannun ka, da shi ka ke rama jifa.”

KAMFANIN MTN ZAI SHIGA GARARI

Kamfanin lambobin wayar selula, MTN ya bayyana cewa soke yarjejeniyar da Trump ya yi, wadda Amurka ta kulla da Iran, zai kawo wa kamfanin matsalar kasa fitar da kudade daga asusun MTN da ke Iran.

Ranar Talata ne Trump ya ce zai sake saka wa Iran takunkumin cinikayya, wanda Amurka ta janye cikin 2015.

Ko a lokacin da aka janye takunkumin dai sai da Trump ya yi ta sukar janyewar da aka yi.

Cikin 2018 da mu ke ciki, kamfanin MTN na Afrika ta Kudu ya cire kudin sa hare Yuro milyan 88, kwatankwacin dala miliyan 104.26 daga kamfaninn MTN na Irancell.

Kamfanin ya kuma ce akwai wasu Yuro milyan 200 da ba a kai ga fitar da su daga Iran din ba.

MTN Ya ce zai ci gaba da sa-ido kan al’amarin.

Share.

game da Author