Shugaban Kungiyar Majalisar Dattawan Arewa, Tanko Yakasai, ya bayyana cewa ba da dadewa ba kungiyar su za ta shirya gagarimin taron makomar siyasar yankin.
Taron, kamar yadda Yakasai ya bayyana, zai kunshi ‘yan siyasar yankin Arewa ne daga bangarori daban-daban.
Ya yi wannan bayani ne jiya Laraba a lokacin da kungiyar ta su ta kai ziyara ga Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.
Yakasai ya ce taron gangamin zai yi magana ne a kan wasu matsaloli da aka san sun addabi Arewa.
Daga nan sai ya roki Majalisar Dattawa da ta goyi bayan taron tare da goyon bayan gudanar da shi.
Yakasai ya shaida wa Saraki cewa sun akai masa ziyarar ce domin su sanar da shi dalilin kafa kungiyar, manufofin ta da kuma muradin da ta ke son ta cimma.
Ya ce ba gaskiya ba ne da ake ta yada ji-ta-ji-tar cewa sun je ne domin neman su fito da dan takarar zaben shugaban kasa daya tal. Ya ce su dai su na neman gudummawar hadin kai daga ‘yan Najeriya, masu hangen nesa da kyawawan manufofi.
Saraki ya yaba da kungiyar, kuma ya nuna cewa lokaci ya yi da za a hada kai a samar dauwamammnen zaman lafiya a kasar nan.
Ya ce a matsayin su na shugabanni kuma ‘yan siyasa, akwai nauyi kan su wajen samo hanyoyin da za a warware matsalolin da ke kawo wa kasar nan tarnakin ci gaba.
Ya jaddada cewa tabbas akwai matsaloli, kuma dama an ce barin abinci a ciki ba a maganin yunwa.
Daga cikin wadanda suka kai wannan ziyarar, akwai Tanko Yakasai, Ibrahim Mantu, Haliru Mohmmed, Babangida Aliyu, Idris Wada da BalaMohammed.
Akwai kuma Zainab Maina, Inna Cirma, Umar Ardo da Joseph Waku.
Discussion about this post