A yau Alhamis ne aka gurfanar da Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan sandan Najeriya, Sunday Ehindaro, tare da tsohon Kwamishinan ‘Yan sanda John Obaniyi a kotu.
An gurfanar da su ne a Babbar Kotu da ke Apo, Abuja, inda ake zargin su da laifin zambar kudade har naira milyan 578, wadanda gwamnatin jihar Bayelsa ta bayar a matsayin gudummawa domin a sayo makamai.
A cikin takardar tuhumar da ake yi musu, mai gabatar da kara ya ce su biyun sun karkatar da kudaden zuwa cikin asusun ajiyar su na banki, inda ba da dadewa ba aka samu kudaden ruwa na ladar ajiya, har naira milyan 16,412,315.
An ce su ma kudaden ruwan wadanda ake zargin ne su ka yi amfanin kan su da kudaden.
Ana kuma zargin su da sheka wa jami’an hukumar ICPC karya cewa wai sun yi amfani da kudin ruwan a hanyar da ta dace, alhali kuwa ba haka ba ne.
Wadanda ake zargin dai sun ce ba su aikata laifin da ake tuhumar su ba.
Tun cikin 2012 ne aka fara maka Ehindero da Obaniyi kotu, amma su ka shigar da karar da ta sa aka dakatar da ci gaba da shari’ar.
Sai dai kuma cikin Disamba, Kotun Koli ta bada sanarwar a ci gaba da shari’ar kawai.
Bayan mai shari’a ya gama jin jawaban bangarorin biyu, ya daga shari’ar zuwa ranar 29 Ga Yuni, 2018.