Majalisar Tarayya ta amince da rahoton Kwamitin Sauraren Koke-koken Jama’a, inda nan take ta nemi Sufeto Janar na ‘Yan sanda Idris Ibrahim da ya umarci Jami’an ‘Yan sanda su bude kuma su fice daga Hedikwatar Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya, ‘Peace Corps’ da ke Abuja.
Majalisar na so jamai’an tsaro su bude hedikwatar da suka garkame nan da kwanaki 21.
Kwamitin Majalisa ya gabatar da rahoton sa bayan binciken sauraren ra’ayoyi dangane da rufe hedikwatar da suka ce ‘yan sanda sun yi ba bisa ka’ida ba.
Ofishin dai ya na kan Iya Abubakar Crescent, a kan babban titin Alex Ekweme Street, ya na kallon Jabi Lake a Abuja.
‘Yan sanda sun kulle ofishin tun a ranar da aka kaddamar da shi, 23 Ga Fabrairu, 2017.
Cikin watan Nuwamba ne Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bada umarnin a bude ofishin, kuma su biya jami’an zaman lafiya diyyar naira milyan 12.
Sai dai kuma ‘yan sanda ba su bi wannan umarnin ba, kasancewa a kullum akwai motocin su da jami’an su a cikin harabar.
Daga baya wata kungiyar rajin kare hakkin jama’a ta rubuta wa Majalisar Dattawa takardar neman ‘yan sanda su tsame hannun su daga harkokin ‘Peace Corps’.
Shugaban Kwamitin Bincike Hon. Nkem Abonta, daga jihar Abia, ya ce halayyar da ‘yan sanda ke yi ta kin bin umarnin kotu, ya na zubar da kimar dimokradiyyar Najeriya a idon duniya.
Har ma ya kara da cewa ya na da takardun da Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan sanda, cewa ya umarci jami’an sa su fice daga harabar, amma bai bi umarnin ba.