Kungiyar ‘Jama’atul Nasril Islam (JNI) ta bayyana cewa babban abinda zai taimaka wajen hana shigowa da sarrafa maganin Kodin a kasar nan shine idan a ka kafa wata doka mai tsauri da za ta hukunta duk wanda aka samu yana aikata wannan abu a Najeriya.
Shi wannan doka zai taimaka wajen dakile yaduwar magani sannan masu ganin suna cin karen su babu babbaka, za su shiga taitayin su idan har mutum ya san idan aka kama shi zai yaba wa aya zaki.
Sakataren kungiyar Khalid Aliyu ne ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a Kaduna.
” Muna wa Allah godiya yadda gwamnatin tarayya ta hana shigowa da sarrafa wannan magani wato kodin sannan muna kira ga gwamnati da ta samar da doka da zai hukunta duk wanda ya aka samu yana safarawa ko siyar da wannan magani. Domin ya zamo masifa ga musamman Arewa.”
Discussion about this post