Shugaban Hukumar EFCC mai riko, Ibrahim Magu, ya soki kungiyar nan mai bin diddigin tabbatar da gwamnatoci sun yi ayyuka kan ka’ida, wato ‘Transparency International’.
Magu ya nuna rashin amincewa ne a kan jadawalin kasashen da kungiyar ta nuna cewa sun fi baci da cin hanci da rashawa.
Magu ya ce shi dai guiwowin sa ba za su yi sanyi ba daga yaki da cin hanci da rashawa. Don haka, wannan jadawali ba abin dogaro ba ne.
“Akwai siyasa mai yawa a cikin kididdigar ta su da suke yi. Ni ban yin amanna da ita ba. Ban kuma yarda da kididdigar ta su ba.”
Magu ya kara da cewa idan ana maganar yaki da cin hanci a kasar nan a yanzu, to dole a jinjina wa Najeriya, domin a yanzu dai kam ta yi rawar-gani.
“Saboda Allah ku da ke zaune a wannan kasar za ku iya cewa yadda Najeriya ta ke a yanzu, haka ta ke a shekaru 12 da suka gabata?
“Duk da dai ni ban yarda da matsayin da suka dora Najeriya ba, mu na yin bakin kokarin mu don mu ga ko za su kara mana mataki a shekara mai zuwa.” Inji Magu.
Kididdigar da kungiyar ta yi, ta nuna cewa rashawa da cin hanci na kara muni a Najeriya, tsakanin 2016 da 2017.
Rahoton dai ya sa Najeriya a mataki na 148 daga cikin kasashe 180. Hakan na yin nuni da cewa al’amarin ya yi muni kenan sosai, idan aka dubi rahoton 2016 da ya dora Najeriya a mataki na 136 a cikin kasashe 180.
Fadar Shugaban Kasa ma ta yi tir da rahoton, ta ce kirkirar karya ce kawai.
Discussion about this post