WASIKA: Fadar Shugaban Kasa ta maida wa PDP martani

0

Fadar Shugaban Kasa ta maida raddin wasikar da jam’iyyar PDP ta rubuta wa Majalisar Dinkin Duniya (UN), inda ta yi zargin cewa Shugaba Muhammadu Buhari na kokarin karya dimokradiyyar Najeriya.

Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus ya rubuta wasikar, wadda tuni a cikin wani jawabi da Kakakin Shugaban kasa, Garba Shehu ya sa wa hannu, ya kira jam’iyyar adawa ta PDP da cewa shure-shure ne kawai ta ke yi, sai dai ta mutu, amma ba za iya sake dawowa ta sake kassara tattalin arzikin Najeriyar da a baya ta yi kaca-kaca da shi ba.

“Akwai ma abin dariya kamar a ce wai PDP ce za ta kai gwamnatin Najeriya kara cewa za ta lalata dimokradiyya? Wannan ai sun janyo wa kan su abin habaici da ba’a ne kawai.”

A cikin wasikar Secondus, ya ce Buhari na shirin yin amfani da INEC, sojoji da ‘yan sanda domin su karya Najeriya.

Cikin bayanin da fadar shugaban kasa ta fitar,Garba Shehu ya nuna lacca da wa’azin da PDP ke yi a kan dimokradiyya ko APC da cewa abu ne da za a iya kira kalaman tubar-muzuru, amma kuma ga kazar mutane a cikin bakin sa.

Ya ci gaba da cewa yaki da cin hanci da rashawa da wannan gwamnati ke yi, ba za a daina ba, kuma za a ci gaba da gurfanar da wadanda ake zargi. Don haka babu yadda za a yi a kira shi da danne ‘yancin dan Adam.

Shehu ya shawarci shugaban na PDP, Secondus ya sani fa ba zai iya yaudarar ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya ba, domin hukumar sun san abin da suke yi.

“Su fa ‘yan siyasar Najeriya sun saba da handamar kudade iyakar yadda ran su ke so, babu mai taka musu burki. To a yau sai aka samu wani ya hau ya ce shi bai yarda ba, ko kai wane, komai girman ka sai doka ta bi ta kan ka. To kun ga su kuwa ba su saba da irin wannan bin ka’idar ba.” Inji Shehu.

“Ai su fa PDP a baya batun tsaron kasa shi ne babbar hanyar su ta handamar kudade.”

Ya ci gaba da cewa tun daga shugaban PDP Uche Secondus da duk ma wani da ya san ya handama ya dirka cikin sa, to nan ba da dadewa ba doka za ta biyo takan sa, ko ya shirya, ko bai shirya ba.

Share.

game da Author