Yayin da ake ci gaba da zarge-zarge da kala wa mulkin Goodluck Jonathan daka warwason dukiyar kasa, ranar Lahadi kuma Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya warware zare da abawar wasu zarg-zargen satar makudan kudade da ya ce sun wakana a lokacin gwamnatin da ta gabata.
Mataimakin Shugaban Kasa ya kara da cewa wadannan bayanan da ya fallasa, “somin-tabi” kawai.
Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa ne ya buga sunayen da bayanan ranar Lahadi da dare, biyo bayan raddin da magoya bayan Goodluck Jonathan su ka yi masa cewa zargin da ya yi a kan gwamnatin Jonathan duk shirbitsi ne kawai babu wata hujja.
Kakakin Yada Labaran Mataimakin Shugaban Kasa, Laolu Akande, ya aiko wa PREMIUM TIMES bayanan, kuma ya ce ko sau daya Osinbajo bai taba ambatar sunan Jonatahan ya ce ya saci kudade ba, cewa dai kawai ya ke a lokacin gwamnatin sa.
Ga Jawabin Na Osinbajo
“Mun karanta wani raddi da makusantan Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan su ka yi wa Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, inda suka musanta maganganun da ya yi dangane da makudan kudaden da ya ce an sace a zamanin gwamnatin Jonatahn.
“Mai magana da yawun Jonathan ya ce ai dukkan bayanan da ke ta yawo a ko’ina cikin kasar nan, dangane da zargin satar kudade, kai har ma da wadanda ke a gaban kotu da ake tuhume-tuhume duk karya ce kawai aka citsa. Kuma wasun mu da ke cikin gwamnati sun san harka ce ta karya kawai.
‘‘Sun zargi Mataimakin Shugaban Kasa da yi wa tsohon shugaban kasa sharri.
‘‘Kimanin Dalar Amurya biliyan 3 aka sace daga kasar nan a cikin 2013, kuma mutane uku ne kacal su ka sace kudin. A yau kuma dala biliyan 3 ta na kwatankwacin naira tiriliyan 1. Ga shi kuma gaba dayan kasafin kudin Najeriya naira tirilyan 7 bakwai ne.”
Yayin da Akande ya kara bada hasken cewa Osinbajo bai ambaci sunan Jonathan ba, ya ce a yanzu haka a Ingila ana ci gaba tafka bincike kan wadannan makudan kudaden tun cikin 2013.
Akande ya ce an sace kudaden ne daga Hukumar Kula da Harkokin Mai, NNPC. Ya bayyana wadanda ake zargin kwashe kudaden su uku da: Jide Omokore, Kola Aluko da tsohuwar Ministar Man Fetur, Diezani Alison-Maduekwe.
Ya ce kamfanonin Omokore da Aluko ne su ka rika jidar mai su na ficewa da kasashen waje, amma ba su biyan kudaden ga gwamnatin Najeriya.
Kudin Makamai
“An karkatar da kudaden da aka sace kimanin dala biliyan 2.5 da nufin sayo makaman yaki da Boko Haram. Hujjar farko wajen wannan ita ce yadda aka fara binciken wadanda ke da hannu kuma tuni ana ta kwace dimbinn kadarorinsu sannan kuma ana ci gaba da shari’o’in su a kotuna sun a fuskantar hukunci
“An waske da Dala miliyan 289 madarar kudi a ranar 25 Ga Faburairu, 2015 daga asusun hada-ka mai lambar baca 000-0000-11658-366 daga asusun NNPC da ke bankin JP Morgan Chase Bank, na birnin New York, Amurka.
“An sake kamfatar naira biliyan 70 daga asusun tarayya a ranakun 8 Ga Janairu da 25 Ga Fabrairu, 2015.
“An jidi naira biliyan 60 a ranar 25 Ga Agusta, 2014. An raba kudin gida biyu. Biliyan 40 aka fara lodawa, baga baya kuma aka sake dora naira bilyan 20 a kai. Hukumomi biyu ne su ka raba wa kan su kudaden a karkashin kulawar Hukumar Leken Asiri ta Kasa, NSA.
“Akasarin wadannan makudan kudade, duk cikin aljifan ‘yan jam’iyyar PDP suka zurare, wadanda daga cikin su kuwa ana nan ana tatsar wasu da yawa su na maido da wasu kaso daga kudaden. Wasu da daman a fuskantar shari’a a kotu.
Bayan an ci gaba da bayyana wasu sace-sace na kananan kudade daga naira milyan 300 har zuwa bilyan 10 sau wurare da dama, daga nan kuma bayanin ya ci gaba da warware yadda cikin kankanin lokaci aka kusa tsiyata Najeria.
Bayanin ya kuma tunatar da lokacin da Gwamnan Babban Bankin Najeriya na Lokacin, Sanusi Lamido Sanusi, ya fallasa cewa akwai wasu Dala biliyan 20 da ya kamata a ce an ajiye su a bankin na CBN, amma gaba dayan su duk sun yi fikafikai, sun tashi sama.
Wannan fallasar ce sanadiyyar da Jonathan ya yi tabarmar-kunyar cire Lamido daga mukamin sa na gwamnan banki.
“Dala miliyan 289 kacal daga cikin kudaden da suka sace, kwatankwacin naira bilyan 88.1 sun isa a wannan gwamnatin ta yi aikin samar da aikin yin a N-Power ga matasa 244,000 da suka kammala digiri din su a tsawon shekara daya, ko kuma a biya kudaden ciyar da dalibai bilyan 1.2 ko gyaran rabin titin Lagos zuwa Ibadan, ko rabin titin Abuja-Kaduna-Kano.
Daya daga cikin hadiman Goodluck Jonathan, Reno Omokiri, ya yi tir da Yemi Osinbajo, ya na mai cewa mataimakin shugaban kasa ya zama gwanin iya bada labarai na shafa-labari-shuni.
“Lallai su O’o an dai ci baya. Shin ya rasa aikin yi ne ya zubar da girman sa ya koma ya na aikin kakakin yada labaran EFCC ko kuwa? Don me ba zai bari EFCC ta yi aikin ta ba?
“In banda rashin kunya, su ne fa ta su gwamnatin ta cire Dala miliyan 496 wai da sunan cinikin makamai, ba tare da bin ka’ida ba. Duk wadannan makudan kudade fa wai jiragen yaki 12 ne kacal za a sayo da su. Wai kuma su ne ke zargin gwamnatin Jonathan da cirar kudade ba kan ka’ida ba. To su kuma fa?”