
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya kai ziyarar gani wa ido garin Gwaska, inda mahara suka kashe kimanin mutane 58.
Gwamnan ya kuma gana da Sarkin Birnin Gwari, Jibril Zubair II da sauran shugabannin yankunan al’umma kafin ya karasa garin Gwaska, inda aka yi mummunan kisan.
A fadar Sarkin, El-Rufai ya nuna matukar bakin ciki kuma ya yi wa iyalan wadanda aka kashe ta’aziyya.
Ya tabbatar musu da cewa abin ya na matukar damun sa da kuma gwamnatin sa, amma da iznin Allah za a magance wannan harin ta’addanci da al’ummar yankin Birnin Gwari ke fama da shi.
Shi kuma Sarki Jibril Zubair, ya yaba da ganin yadda gwamnati ta kamo hanyar shawo kan matsalar gadan-gadan.
Ya na mai cewa a matsayin sa na daya daga cikin mambobin majalisar tsaro ta jihar Kaduna, ya san irin namijin kokarin da ake a kai yanzu domin magance hare-haren.
A garin Gwaska, wani dakaci mai suna Isa Musa ya zagaya da gwamnan kuma ya ba shi labarin yadda abin ya faru.
“Sun shigo mana dauke da manyan makamai, kuma ba kananan mahara ba ne. Sun kutso ta ko’ina suka kewaye mu su na harbi su na banka wa gidajen mu wuta.
“Mu na godiya da kokarin da ku ke yi, amma fa maganar gaskiya magance wannan matsala fa sai dai zaratan sojoji na kasa da kuma na sama kawai. Rikakkun mahara ne mutanen da ke kashe mu. Domin ai tsakanin mu da Dansadau bai fi kilomita bakwai ba. Ga kuma kan iyakokin Katsina da Nijar duk a nan Birnin Gwari.”
A dalilin haka tuni gwamnati ta amincewa ta kafa bataliyan din Sojojin da na ‘yan sandan a wannan yankin.
Bayan haka wasu mazauna karamar hukumar sun jinjina wa gwamnan da Shugaba Buhari kan shawarar kafa wani sansanin Sojojin a yankin.
” Duk da muna cikin tashin hankali yanzu haka, dole mu yaba was gwamnati sannan mu ci gaba da yin addu’a don samun zaman lafiya na dindindin a wannan yankin.
” A haka har sanatan mu mai jiran gado, Uba Sani ya biyo gwamnan domin ya gani wa idon sa, wannan fa tun kafin ya hau Kenan. Bai riga da ya dare kujerar ba. Ka ga haka nuni ne cewa yana tare da talakawa da mutanen da zai wakilta.
A karshe, sun roki gwamnati da ta taimaka wa ‘yan bangan kauyukan da taimako na musamman domin suna taimaka wajen dakike irin wadannan hare-hare.
Discussion about this post