Gwamna Darus Ishaku na Jihar Taraba, ya bayyana a ranar Alhamis cewa sun a bayan Janar TY Danjuma dangane da furucin sa da ya zargi sojoji na goyon bayan masu kai musu hare-hare.
Wannan hare-haren ne dai ya kai har Danjuma ya ce kowa ya yashi ya kare kan sa, kuma kowa ta sa tafisshe shi tunda jami’an tsaro ba su iya kare rayukan jama’a.
Ishaku ya bayyana haka ne lokacin da kwamitin da gwamnatin tarayya ta nada domin ya binciki zargin da TY Danjuma ya yi wa sojoji. Ya kai ziyara Gidan Gwamnatin Jihar Taraba a ranar Alhamis.
“Mu dai ‘yan jihar Taraba mu na bayan duk abin da TY Danjuma ya furta, da ya ce kowa ya tashi ya kare kan sa.
Darius ya ce a matsayin Danjuma na tsohon babban hafsan sojan kasar nan, kamata ya yi a dubi maganar da ya fada, amma ba a dora masa karan-tsana ba.
Gwamnan ya ce ya na goyon bayan kafa kwamitin kuma zai bayar da dukkan goyon bayan da ake bukata da hadin kai.