Kwatagwangwamar hakkin mallakar ‘ya’ya tsakanin dan Atiku da tsohuwar matar sa

0

Wata sabuwar kwatagwangwamar hakkin mallakar ‘ya’ya ta sake kunno kai tsakanin Aminu Atiku, dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da kuma matar sa da ya taba aure su ka rabu, mai suna Fatima Bolori.

Cikin 2017, PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo muku cikakken rahoton yadda wata kotu a Legas ta kwace ‘ya’yan daga hannun Aminu Atiku, ta maida su ga Fatima, bayan da shi Aminu ya rike yaran a lokacin da suka je hutu gidan sa, ya ki maida su a hannun tsohuwar matar ta sa.

A wannan karo kuma, ba Aminu ne aka kai kara kotu ba. Shi ne ya sake shigar da wata kara a Babbar Kotun Igbosere da ke Legas, inda ya daukaka karar hukuncin da aka yanke wanda ya ce waccan kotun ba ta yi masa adalci ba.

Aminu a wannan karon ya na kalubalantar kudin ciyarwa har naira N250,000 da kotu ta yanka masa cewa ya rika biyan Fatima tsohuwar matar sa a matsayin kudin ciyarwar ‘ya’yan sa guda biyu.

Baya ga wadannan zunzurutun kudi, kotun ta ce duk wata rashin lafiya da ta samu yaran, to Aminu ne zai biya kudin magani.

Cikin karar da Aminu ya daukaka, ya nemi babbar kotun ta soke hukuncin da kotun majistare ta yanke wanda ta damka hakkin kula da yaran a hannun mahaifiyar su Fatima. Sannan kuma ya nemi a soke wadannan kudi har naira 250,000 da kotun majistare ta ce ya rika biya a matsayin kudin ciyarwa da shayar da yaran su biyu.

Aminu ya na so Babbar Kotu ta maida yaran a hannun sa, ba hannun mahaifiyar su ba.

Aminu ya shaida wa Mai Shari’a Kazeem Alogba cewa kotun majistare ta yi watsi da ‘yancin sa domin ba ta yi masa adalci ba, ta yadda kotun ta goyi bayan Fatima Bolori, tsohuwar matar sa, har ta yanke hukuncin damka mata yaran.

Wata Kotun Majistare da ke unguwar Tinubu a Legas ce dai a cikin watan Janairu ta damka hakkin kulawa da Ameera mai shekaru 11 da Aamir mai shekaru 7 ga mahaifiyar su Fatima.

Lauyar Aminu Atiku mai suna Oyinkan Badejo ce ya shigar da karar a madadin shi mai karar.

A cikin kotun, Badejo ta yi ta bayyana yadda kotun majistare ta yi gaggawar yanke hukunci ba tare da ta saurari wanda ta ke karewa a tsanake an yi masa adalci ba.

Sai dai kuma lauyoyin Fatima su ma sun bude wuta inda suka maida wa lauyar tsohon mijin na ta martani a gaban alkali.

Mai shari’a ya daga karar zuwa ranakun 17 Mayu, da 24 Ga Yuni, 2018.

Share.

game da Author