Haidar Zango ya bi sahun mahaifin sa, ya tsunduma harkar waka

0

Babban dan shahararren mawakinnan sannan jarumin wasannin fina-finan Hausa, Adam Zango, Haidar Zango ya bi sahun mahaifin sa a harkar yin wakoki da fina-finai.

Haidar dan shekara 11 zai saki album din wakar sa ta farko nan ba da daewa ba.

Kamfanin White House Family ne, mallakar mahaifin sa ne suka shirya wannan sabbbin waka da Haidar zai saki.

Bayan haka zango ya rada masa suna na gayu, ‘Star Boy’ wato ‘ Yaro mai Shanawa’.

Wata mai yin fashin baki a harkar fina-finai da shakatawa ta shaida mana cewa lallai tayi farincikin haka da Adamu yayi sai dai tana bashi shawara da ya fi ba da fifiko wajen ganin yaron ya samu karatu na zamani sosai.

” Idan ba a manta ba Zango ya kan fito ya fadi cewa shi bai yi makarantar boko ba, yana korafi kan yadda ake gyara masa rubutun turancin sa. Wannan dama ce ya samu da zai tabbatar ya ga cewa dan sa Haidar ya wuce nan.

Da yawa daga cikin masoyan sa sun yi ta tofa albarkacin bakin su, suna ya wa Haidar fatan alkhairi a abin da ya sa a gaba.

Share.

game da Author