Ware isassun kudade ne mafita ga matsanancin zazzabin cizon Sauro da ake fama da shi a kasashen duniya

0

Shugabanin kasashen duniya, manyan ‘yan kasuwani na duniya, likitocin kimiya da kungiyoyi za su yi zama na musamman domin kirkiro hanyoyin da za a Iya bi domin kawo karshen cutar zazzabin cizon sauro a kasashen dake fama da shi duniya.

Kungiya mai zaman kanta ‘Ready to Beat Malaria’ ta sanar da haka inda ta bayyana cewa gwamnatin kasar Britaniya, Rwanda da Swaziland ne suka shirya wannan taron da za ayi a birnin Landon.

” Mun kuma hada guiwa da gidauniyar Bill da Melinda Gates domin ganin an sami nasarar kawar da cutar zazzabin cizon sauro a ko ina a fadin kasar nan.

Kungiyar ta ce bincike ya nuna cewa a shekarar 2000 cutar ta yi ajalin miliyoyin mutane da suka kamu da cutar.

” Cutar zazzabin cizon sauro ya karu ne a dalilin yawan rikice-rikice da akayi ta samu,rashin ware isassun kudade domin kawar da cutar,canjin yanayi da hakan ya sa aka samu yalwatar sauro a garuruwan da birane.

” Da dala tiriliyan 4 za a iya kare miliyoyin mutane daga kamuwa da cutar daga nan har zuwa 2030.”

Share.

game da Author