An damke masu garkuwa da mutane da suka addabi mutane a Jihar Katsina

0

Rundunar ‘Yan sandan jihar Katsina ta bada sanarwar damke wasu masu garkuwa da mutane su takwas da suka addabi kananan hukumomin Danja da Kafur da cikin jihar Katsina.

Kakain rundunar ‘yan sandan jihar, Mataimakin Sufurtanda Gambo Isa, ya ce an kama Joshua Yohanna, Musa Ibrahim, Nafiu Umar da Kabir Lawal a yakin karamar hukumar Kafur.

Ya ce wadannan su hudu din ne suku buga wa Haruna Bello da Nuhu Yusuf, mazaunan kauyen Gozaki cewa ko dai su aiko musu da naira milyan 3, ko kuma su kashe su idan sun yi garkuwa da su.

“Wadanda aka yi wa barazanar kisan har sun kai ga aikawa da naira dubu 300, kafin su sake hada kudi su tura ciko, sai kuma su ka canja shawara, suka shaida wa ‘yan sanda.

“Nan da nan jami’an tsaro su ka gaggauta kamo su, inda suka tabbatar wa jami’an bincike a ofishin ‘yan sanda cewa tabbas sun aikata laifin.

‘Yan sanda sun yi nasasar samun layin wayar selula da masu garkuwar suka yi amfani da ita suka kira wadanda suka yi wa barazanar.

Ya kara da cewa an kuma an kama wasu masu garkuwa da mutane su hudu da suka hada da MuBARAK Babangida, Abubakar Lawal, Aliyu Lawal da Nuhu Abdulhamid.

Su kuma wadannan an kama su ne a Katsina sun yi shigar mata, a lokacin da suke kokarin sake wani karamin yaro mai shekaru hudu.
Dukkan su za a gurfanar da su a kotu.re

Share.

game da Author