Tunda Buhari ya nuna min halin ko-in-kula, Zan canza kasa kawai – Malamin Kwalejin Fasaha

0

Wani malami da ke koyarwa a Babbar Kwalejin Fasaha ta Akanu Ibiam da ke Jihar Ebonyi, ya yi barazanar ballewa daga Najeriya idan gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta gaggauta bi masa hakkin dankwafe shi da ake yi ana hana shi ci gaba ba.

Malamin mai suna Victor Koreko, wanda be fannin nazarin fasahar kirkirar kayan karau da gilasai, ya bayyana wa PREMIUM TIMES a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi cewa, ana nuna masa bambanci da tsana, yadda ta kai shekaru takwas kenan an ki a kara masa girma ko mukami.

Malamin wanda ya zargi hukumar makarantar da cin hanci, an tambaye shi to wace kasa zai koma idan ya balle daga Najeriya, sai ya ce, shi ba zai koma kowace kasa ba tukunna, domin bas hi da wata kasar da ke zuciyar sa a halin yanzu. Amma duk da haka ya bayar da amsar inda zai koma na wucin gadi.

“Da farko zan fara tsayawa ne a karkashin Hukumar Kwatar ‘Yancin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya bayan na fice daga Najeriya. Zan zauna ne ba ni da wata kasa a duniya kaf, kafin daga baya na yi nazari.

Dama dai can baya PREMIUM TIMES ta taba buga wasikar da ya rubuta wa Shugaban Kasa ya na neman janyewa daga Najeriya, ya kasance shi ba dan Najeriya ba ne.

Share.

game da Author