ROKO: Ku rage tsawwala wa mutane kudin magani a asibiti masu zaman kan su- Aisha Buhari

0

Uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi kira ga asibitoci masu zaman kan su da su rage tsawwala wa mara sa lafiya kudin neman magani idan suka zo asibitoci irin wadannan.

Aisha ta yi wannan kira ne a fadar shugaban kasa da take karbar bakoncin kungiyar likitocin dake aiki a asibitocin gwamnati da masu zaman kan su.

Aisha ta ce rage farashin kudin asibitin da asibitoci masu zaman kan su za su yi zai taimaka wa mutane musamman talakawa samun ingantaciyyar kiwon lafiya sannan da bunkasa ingancin kiwon lafiya a kasar nan.

” Saboda haka ne ina kira ga kungiyoyi masu zaman kan su a kasar nan da su hada hannu da gwamnati wajen yin zubin da zai bunkasa fannin kiwon lafiya don rage wa gwamnati nauyi.”

A Karshe ta yi kira ga likitocin kasar na da su riki aikin su da muhammanci da kula sannan su nisanta kansu daga cin hanci da rashawa.

Share.

game da Author