Kashe-kashe a Najeriya laifin Gaddafi ne – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya dora laifin kashe-kashen da ke faruwa a fadin kasar nan a kan tsohon shugaban Libya, Mu’ammar Gaddafi.

Gaddafi, wanda tunzurin ‘yan tawayen kasar ya yi sanadiyyar ajalin sa cikin 2011, Buhari ya ce shi ne silar kashe-kashe a wannan shiyya ta tsakiyar Najeriya.

An kashe Gaddafi cikin watan Oktoba, 2011, bayan ya shafe shekaru 42 ya na mulki.

Rahotanni sun nuna cewa yayin da ‘yan tawaye tare da goyon bayan Turawa da Amurka suka mara wa masu tawayen baya, shi kuma Gaddafi ya raba wa magoya bayan sa makamai,wanda hakan ya yi sanadiyyar jefa kasar cikin mummunan yakin basasa har na tsawon shekaru bakwai.

Yayin da Buhari ke bayani tare da Babban Bishop na Canterbury, Justin Welby a ranar Laraba, ya yi ikirarin cewa makaman da Gaddafi ya jibga wa magoya bayan sa ne aka rika yin watandar su a Arewa ta tsakiyar kasar nan.

“Matsalar dadddiya ce, ta ma girme mana. Amma dai shigo da muggan makamai da kutsen da mahara suka rika yi daga yankin Sahel zuwa cikin kasashen Afrika ta yamma.”

“Gaddafi ne ya rika bai wa wadannan mahara makamai kuma ya na yi masu tirenin na horaswa. Bayan da aka kashe shi, sai suka rika tserewa da makaman da ke hannun su. Mun sha arangama da irin su su na taya Boko Haram fada.

“Makiyaya da aka sani ba su rike komai sai sandar kiwo da adda idan ta kama domin saran ganyen da dabbobi za su ci ko buda wa dabbobin su hanya a cikin surkukin jeji, amma an wayi gari su ne ke daukar muggan makamai.” Inji Buhari.

Ya kara yin watsi da zargin da wasu ke yi cewa kashe-kashen na da nasaba da kabilanci ko addinanci, ya ce masu wannan ra’ayin su na yi ne don siyasar kan su kawai.

Sai dai kuma wani wani masanin matakan tsaro mai suna Mike Ejiofor, wanda tsohon daraktan hukumar tsaro ta SSS ne, ya ce, ‘‘Abin takaici ne shugaban kasar mu ya fita can wata kasa ya na babatun bayyana musu cewa ‘yan ta’addar mu daga Libya su ke. Ba mu fa da kan iyaka da Libya, kuma idan za a yi nazari, za a ga sauran kasashen da ke makwautaka da Libya ai ba su fama da irin wannan kashe-kashen.’’

Share.

game da Author