Ta kacame tsakanin sanatoci bayan wani ya soki Buhari

0

Rikici ya kaure yau a Majalisar Dattawa, bayan da Sanata Enyinnaya Abaribe, ya ragargaji Shugaba Muhammadu Buhari har ta kai ga ya kira shi ‘wanda bai cancanci rike shugabanci ba.’

Abaribe ya tashi ya kawo batun matsalar tsaro a kasar nan da ya nemi a tattauna ta, amma sai bayanan da ya gabatar ya hargitsa zauren majalisar.

Dama ko a cikin watan Maris, sai da Sanata Abaribe ya ragargaji Buhari, ya ce shugaba ne da ba ya yarda ya yi kuskure, sai dai ya dora laifin akan wani can.

“Jama’a ku saurara, jiya a Landan Shugaba Buhari ya dora wa marigayi Gaddafi laifin kashe-kashen da ake yi a kasar nan, kuma ya ce bakin-haure ne ke kashe mutane. To hakan ya yi daidai da batun da na yi kwanan baya inda ga shi Buhari, a matsayin sa na Babban Kwamandan Askarawan Kasar nan baki daya, ya nuna cewa ba ya iya kakkabe kashe-kashen bakin-haure. To idan haka ne, mene ne amfanin sa kenan a kan mulki?

“Shikenan za mu ci gaba da kasancewa a karkashin wannan shugaba wanda duk abin da ya tabka zai fita kasar waje ya nuna wa duniya cewa shi bai iya shugabanci ba ne…?”

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya taka masa burki bayan da ya ga sanatocin APC sun dirar wa Abaribe da hayaniya wuri ya hargitse.

“Ka yi wa mutane shiru, ka rufe mana baki, ba za mu bari ka karasa bayanin ka ba.” Haka sanatocin APC suka rika cewa, suna nuna wa Saraki ya taka masa burki.

Bayan an dan yi tsit, sai Shugaban Masu Rinjaye, Ahmed Lawan ya nemi Abaribe da ya janye furucin da ya yi kan Buhari.

Amma Abaribe ya tsaya tsayin daka ya ce ba zai ba kowa hakuri ba, daga Shugaba Buhari din har Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki. Daga nan ne kuma ya kara harzuka sanatocin da suka nemi ya janye maganar.

Haka aka shafe tsawon lokaci ana hargowa da hatsaniya a zauren majalisar.

Sai da Saraki da kan sa ya sa baki ya nemi Abaribe ya janye Bayanin da ya yi, sannan ya hakura ya janye.

“ Shugaban Majalisa ina ganin girman ka. Amma fa ni ban ga wasu kalmomin da zan bayyana abin da Shugaba Buhari ya yi idan ba yadda na bayyana su din ba. Shi ya yi wannan bayani a Landan. Amma ina bada hakuri idan ba a fahimci abin da na ke nufi ko na ke bayani a kai ba. Shi da kan sa ne ya yi ta maganganu barkatai a kan kashe-kashen da ake yi a Najeriya.”

Share.

game da Author