RIKICIN BENUWAI: Sojoji sun kashe mahara hudu, sun kwato makamai

0

Rahotanni sun tabbatar da cewa sojoji sun kashi wasu mutane a cikin karkarar yankuna a jihar Benuwai, a cikin 2018 da kuma wasu jihohi da ke makwautaka da jihar.

Rikicin dai na yankin na ci gaba da ruruwa duk kuwa da girke sojoji da aka yi a jihar da kuma ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai jihar.

Sai dai kuma a cikin makon jiya ne Buhari ya danganta wannan rikici da sojojin haya daga Libya, bayan da aka hambarar da Gwamnatin Mu’ammar Gaddafi.

A yau Talata rundunar sojoji ta bayyana cewa an yi arangama tsakanin sojoji da mahara a kauyen Teguma, cikin karamar hukumar Guma ta Jihar Benuwai a lokacin da sojojin ke sinriti.

TEXAS Chukwu, wanda shi ne daraktan huda da jama’a da yada labarai, ya ce an samu bindigogi samfurin AK 47 guda hudu, albarusai da dama.

Chukwu ya ce sojoji za su ci gaba da aikin zakulo batagari a duk inda su ke.

Share.

game da Author