‘Yan sanda sun damke wata ‘yar kunar bakin wake a Maiduguri

0

Dakarun ‘Yan sandan jihar Barno sun kama wata ‘yar kunar bakin wake a sansanin
‘yan gudun hijira dake Bakassi a Maiduguri.

Jami’in harka da jama’a na rundunar Edet Okon ya sanar da haka ranar Talata inda ya bayyana cewa dakarun su sun kama ‘yar kunar bakin wake mai suna Zara Idris ne tana gararamba a cikin sansanin da misalin karfe 6:50 na yamma.

Bayan sun kamata ne suka kwance wannan jigida na bam dake kwankwason ta.

Okon ya yi kira ga mutanen garin da su ci gaba da harkokin su cewa jami’an tsaro za su ci gaba da maida hankali wajen samar musu tsaro.

Share.

game da Author