Ba za mu mara muku baya ba – Kungiyar likitoci ga Kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya

0

A yau Talata ne kungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta bayyana cewa baza ta mara wa kungiyar ma’aikatan Kiwon lafiya na Najeriya (JOHESU) baya ba a yajin aiki da suke shirin fara yi.

Shugaban kungiyar NMA Mike Ogirima ya sanar da hakan inda ya zargi kungiyar cewa an kafa ta ne ba bisa ka’ida ba.

A dalilin haka Ogirima ya yi kira ga gwamnati da ta yi kunen uwar shegu da bukatun da kungiyar na JOHESU me korafin a biya musu.

” Na tabbatar da cewa kungiyar JOHESU ta yi barazanar gudanar da wannan yajin aikin gama garin ne domin ta bakanta mana rai muna.

Idan ba a manta ba jiya litini ne kungiyar JOHESU ta yi wa gwamnati barazanar fara yajin aikin gama gari ranar Talata.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Ogbonna Chimela, ya ce, wa’adin da Kungiyar taba gwamnati ya cika cif a daren litinin din nan ne.

Ya ce muddun gwamnati bata ce komai akai ba toh zasu rufe asibitoci gaba daya sannan duk sauran mabiyan su a jihohi ma za su bi sahu.

Sai dai kuma Ministan Kiwon Lafiya Isaac Adewole ya ce gwamnati na ta fadi-tashi don ganin Kungiyar bata Kai ga far yajin aikin ba

Share.

game da Author