Kotu a tsare wadanda su ka azabtar da jaki a Sokoto

0

Wata Kotun Majistare a Sokoto, ta bada umarnin a tsare wasu matasa Abdulkarim Muhammad da Ibrahim Ibrahim, saboda zargin su da ake yi da laifin azabtar da wani jaki wanda ba na su ba.

Laifi biyu ake cajin su da shi, na farko hada kai su dauki jakin da ba a ba su ba suka je suka hau, sai kuma laifin azabtarwa.

Su biyun dai sun ce ba su aikata abin da ake zargin su aikata din ba.

Alkali Bello ya ce a ci gaba da tsare su har zuwa ranar 24 Ga Afrilu, 2018.

Tun da farko, mai gabatar da kara, Monday Kennedy, ya shaida wa kotu cewa wadanda ake zargin sun hau jakin ne a unguwar Tafawa Balewa da ke cikin Sokoto. Wanda jakin kuma na wani mai suna Faruq Koko ne mazaunin kauyen Mabera.

Ya shaida wa kotun cewa sun hau jakin su na azabtar da shi har sai da suka cimma unguwar Tamaje, inda a can kuma bayan galabaitar da jakin, sai suka damka shi ga wani mai suna Abdulmumin.

“Bayan Abdulmumin ya hau jakin, su na cikin tafiya sai mota ta banke su, shi da jakin duk suka ji raunuka.

“Mai jakin ne da kan sa ya kai kara ga ‘yan sanda a ranar 16 Ga Afrilu, a ofishin mu da ke Unguwar Rogo.

Kennedy mai gabatar da kara ya ce laifin ya saba wa dokar kasa ta Sashe na 97 da 208.

Share.

game da Author