A gaba na Maryam ta far wa Bilyamin da wuka, kwalabe a daren da aka yi kisan – Mai ba da shaida

0

Wani mai ba da shaida a shariar Maryam Sanda da ake zargin ta kashe mijin Bilyaminu Halliru, ya bayyana wa kotu cewa a gaban sa Maryam tayi ta kai wa mijin ta Bilyaminu hari da makamai dabam-dabam yana raba su kafin daga karshe yaji ai ta ma kashe shi.

” Ina gidan Bilyamin muna kallo a falo, sai Maryam ta kira shi sama in da dakin ta yake, ba a dade ba sai gashi ya sakko ya zauna muka ci gaba da kallon mu. Can sai ta sake lekowa da kanta ta kira shi sama. Da ya tafi can ne fa sai naji ‘yar hayaniya.

” Daga nan sai na haura saman domin ganin me ke faruwa. A nan ne na gan su sun shake juna, tana ce masa lallai sai ya sake ta. Da na shigo dakin sai na yi kokarin raba su. Ana haka ne fa sai kawai muka ji fussss, ta fasa kwalban mai ta nufu shi da shi. Nan dai muka yi kokari muka kwace kwalban.

” Maryam tayi ta cewa muddun bai sake ta a wannan lokaci ba tabbas sai ta yanke masa mazakutan sa. Shi kuma yayi banza da ita. Bamu ankara ba kuma sai ta sake daukar kwalban turare ta fasa ta nufe sa da shi. Anan ma Allah ya sa muka kwace kwalban, ita ko sai cewa take “sai ka sake ni ko in yi maka illa”.

” Bayan mun sauko kasa mun zauna sai ta shiga kicin ta dauko sharbebiyar wuka ta nufu shi. A wajen kwace wukan sai ta cije shi a hannu.

“Bayan haka sai Bilyamin ya kira wani dan-uwan sa ya zo gidan. Bayan ya zo ne ya tattauna da su gaba daya sai muka fita tare da yake dare yayi. A cikin mota sai nake bashi bakon labarin abin da ya faru a gidan.

Safiya nayi kuwa sai kanin Bilyaminu ya kira ni ya fada mani cewa Allah yayi wa Bilyaminu rasuwa.

” Da na tafi asibitin sai naga gawar Bilyaminu a kwance, da dabar wuka a tsakiyar zuciyar sa, da shaidar cizo a cikin sa da kuma yankan wuka a matse-matsin sa.

Mai bada shaida ya ce bai ji inda Maryam ta ce za ta kashe Bilyamin ba sai dai tabbas ya ji tana rantsewa sai ta yanke masa mazakutan sa.

Share.

game da Author