Ko ka san rashin yawaita shan ruwa na illata koda? Nisan ta kan ka daga wadannan abubuwa 7

0

Kamar yadda aka sani cewa cutar koda cuta ce dake kama kodar mutum da idan ba an gano da wuri ba ne, ya kan yi ajalin wanda ya kamu da ita.

Koda a jikin mutum na taimakawa wajen tace abubuwan da jiki baya bukata daga jini kamar fitsari, zufa, da wasun su.

Wasu masanan wannan cuta sun gano cewa akwai wasu ababen da mutane kan aikata wanda kan sa a kamu da cutar da ke illata koda.

Wadannan abubuwa sun hada da;

1. Rashin shan ruwa akai-akai.

2. Yawan cin gishiri danye ko dafafe a cikin abinci.

3. Yawan shan barasa (giya)

4. Yawan rike fitsari a mara

5. Yawan shan magunguna musamman magungunan dake taimakawa wajen kawar da gajiya a jiki.

6. Cin abincin dake dauke da sinadarin ‘Protein’ kamar su kwai, kifi, madara,wake da sauransu.

7. Cin abincin dake dauke da sinadarin ‘Caffine’ kamar su goro, taba, bakin shayi wato ‘Coffe’.

Share.

game da Author