Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa za ta zuba idanu da jami’ai sosai domin ta tabbatar da cewa babu wani dan siyasa ko dan koren ‘yan siyasar da ya je rumfunan zabe dauke da kudade ya na rabawa a lokacin zaben gwamnan Ekiti a ranar 14 Ga Yuli, 2018.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaben na Kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne da kan sa ya bayyana haka, kuma ya yi kakkausar gargadi ga jam’iyyun siyasa da su guji sayen masu jefa kuri’a a lokacin zabe.
Ya ce duk wanda aka kama ya na watandar kudade a rumfunar zabe ko a ranar zabe, to zai dandana kudar hukuncin da mai shari’a zai yanke a kan sa.
Yakubu ya yi matumar nuna bacin ran sa ganin irin yadda aka yi amfani da tsabar kudi a lokacin zabukan gwamnonin jihohin Edo, Ondo da Anambra, ta yadda wasu har naira dubu biyar-biyar (N5000) su ka rika rabawa.
Shugaban na INEC ya yi wannan kakkausan gargadi ne a wurin taron masu ruwa da tsaki a kan aikin Cigaba da Rajistar Zabe a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti. Ya ce Hukumar sa za ta hada karfi da jami’an tsaro domin ta tabbatar ta hana harkallar sayen cinikin masu jefa kuri’a a ranar zabe a rumfunan zabe.
Taron dai ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Ekiti, wanda kuma shi ne dan takarar zaben gwamna na jam’iyyar PDP da sauran wasu shugabannin jam’iyyun siyasa, jamai’an tsaro, kungiyar mata ‘yan kasuwa ta jihar da kungiyoyin sa kai da sauran su.
Shugaban Zabe Shiyyar Oyo, Ekiti, Osun da Ondo ne, Farfesa Prince Addeji Soyebi ya wakilci Shugaban Zabe na Kasa. Ya kara yin gargadin cewa:
“Ba za mu bari kowace mota ta matsa kusa da rumfar zabe ba, saboda ‘yan siyasa kan boye kudade a cikin mota. Ta haka ne za mu iya rage yadda ‘yan siyasa ke yawo kudi niki-niki a cikin aljifan su.”
Discussion about this post