TAMBAYA: Menene Hukuncin Musulmi ya auri wadda ba musulma ba? Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Menene Hukuncin Musulmi ya auri wadda ba musulma ba kuma su rayu bata musulun ta ba?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Hakika ya halatta Musulmi ya aure Ahlul-Kitabi, wato kirista ko bayahudiya, mai mutunci da kamun kai, ba fisika ba kuma ba mai alfasha ba. Wannan nassin Alkur’ani mai Girma ne a cikin sura ta Biyar aya ta Hudu. Amma barin aurensu yafi alfanu fiye da auren nasu.

Kuma Alkur’ani ya haranta auren duk matar da ba Ahlul-Kitabi bace kamar mai bautar Gunki, ‘yar addinin Hindu, Buda, me bautar wuta da sauran kafirci.

A karshe lallai mu yi taka tsansan da yin auratayya barkatai batare da kula da Akidar musulunciba. Hakan hadari ne ga mazajen da kuma zurriyarsu.

Allah ka tsare mana Imanin mu da mutuncin mu. Amin.

Share.

game da Author