Tun bayan da Gwamnatin Tarayya a ta bakin Ministan Yada Labaran ta, Lai Mohammed, ya fara fitar da jerin sunayen wadanda ake zargin sun wawuri kudade a zamanin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, ’yan Najeriya sun rika tofa albarkacin bakin su. Yayin da wasu magoya bayan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke murna da ganin jerin sunayen, wasu kuma cewa suke yi ai tuni ake yi musu irin wannan tatsuniyar.
Akwai kuma masu cewa su ba su ga dalilin fitar da sunayen ba, domin an saba jin wannan zance, kuma dama ai ita APC, tun ma kafin ta hau gwamnati ta ce ta san an tafka barna, don haka ta zo ne don ta yi gyara.
Da dama na korafi kan APC cewa maimakon gwamnati Buhari ta dukufa ta na gyara, kullum sai bada labarin barnar baya ta ke yi. Wasu na ganin cewa ai babu narabar dambe da fada idan ana maganar PDP da APC ne.
A Abuja da kewaye ba z aka san ana siyasa ba sai idan ka ga matasa sanye da jar hula, wadda ke tabbatar maka da cewa mabiyar darikar Gidan Kwankwasiyya ne.
Amma a ranar Asabar da ta gabata, na je hutun-ganin-gida a Kano. Tun ban kai ga warwarewa daga gajiyar tuki da bugun ramuka daga Abuja zuwa Kano ba, na fahimci lallai siyasar Kano na ci gaba da zafi, musamman irin yadda na rika jin ra’ayoyin jama’a dangane da jerin sunayen da Gwamnatin APC ta fitar na wadanda ta ce su ne suka sace dukiyar al’umma a zamanin mulkin PDP a karkashin Goodluck Jonathan.
NI DA MAKWABCI NA
Aliyu Nasiru mazunin unguwar Karkasara a Kano, kuma ba shi da nisa da gida na. Na zo wucewa sai na iske sun rukume da gardama, inda shi ya ke cewa, “ya kamata fa kowa ya fahimci cewa APC gwano ce, wanda ba ya jin warin jikin sa, sai warin jikin PDP kawai ta ke ji.
“Idan ba haka ba, ka duba ka gani, ita APC a yanzu ta na ta ba mu labarin satar da aka yi lokacin gwamnatin Jonathan. Amma kuma wadanda suka wawure kudaden kasar nan da tuni EFCC na shari’a da su, duk su na cikin APC, da su ta kafa gwamnati.
‘‘Ina irin su Danjuma Goje? Ina Saminu Turaki da ake neman naira biliyan 40 a hannun sa? Su da sauran gaggan PDP na gwamnatin Obasanjo da ta Umaru ‘Yar’Adua duk fa su na cikin jam’iyyar APC.
TSAKANIN LABARAN DA CHIDOZIE
Na shiga Kasuwar Sabongari domin sayen wasu ‘yan kayan amfani a gida. A kusa da kantin da na ke sayen kaya, makwabcin mai kantin, Chidozie Obinna, mai sayar da kayan shafe-shafe a cikin Kasuwar Sabon gari, Kano, ya rika kushe sunayen yayin da Alhaji Labaran wanda na je wurin sa ke kare gwamnati. Chidozie cewa ya yi, shi fa duk wani abin da gwamnatin APC za ta fada, jin sa kawai ya ke yi, amma kame-kame kawai su ke yi.
“Mun ji an saci kudi a lokacin Jonathan. Abin da mu ke nema ga wannan gwamnatin shi ne ta bayyana mana nawa ta kwato, kuma wadanne ayyuka aka yi da kudaden? Ko su daure wadanda su ka kama, ko kada su daure su, wannan kuma ruwan gwamnatin, tunda dama idan ka duba, za ka ga da PDP da APC,su ya su duk daga ‘yan uwa sai ‘yan gari daya sai kuma surukai da abokanai da ‘ya’yan dangi.
“A kullum cikin kasuwar nan ba ka jin komai sai gardamar siyasa, musamman idan ana rashin ciniki kowa ba shi da aikin yi. To na yi nazari, a lokacin da Jonathan ke mulki, har ya sauka sabulun Tura guda daya bai kai naira 300 ba. Amma a yau, idan ka bude super market, sai ka sayar da sabulu daya tal naira 800 sannan za ka iya cin ribar naira 50. To me wani zai zo a yanzu kuma ya gaya min har na tsaya na saurare shi?
Da yawan wadanda na rika ji suna bobbotai, sun nuna cewa ya kamata Lai Mohammmed ya lissafa manyan ‘yan PDP da suka koma APC aka kafa mulki da su, kuma suka rika babbaka gobarar kisan makudan kudade ga APC a lokacin kamfen.
Wasu kuma na yin korafin cewa dukkan gwamnoni da tsoffin sanatoci da gwamnonin baya, sun rika kashe wa APC kudade, alhali kuma kowanen su ba saye da sayarwa ya ke yi ba, a hantsar gwamnati ya ke tatsa, su sha kuma su yi wa jam’iyya hidima da kudaden.
NI DA ABOKI NA A TITIN ZOO ROAD, KANO
A kan titin Zoo Road kuma na tsaya sayen doya, na ci karo da wani da muka dade ba mu hadu da juna ba. Bayan mun gaisa, sai na tambaye shi labarin gari. Maimakon ya amsa min, sai ya far aba ni labarin matsalar gari. “Ce mana su ka yi idan Buhari ya hau zai dawo da dalar Amurka daidai da naira. Haka Buharin kan sa ya fada, kuma kowa ya sha ji. Amma ga shi har sun fara kamfen na tazarce a fakaice, har yanzu dala daya tal ta na daidai da naira 360.
“A haka kuma wai wani dan boko zai rika ce mana wai wannan gwamnati na gina tattalin arziki. Ta ina zai ginu dala ta yi wa naira fintinkau? Inji Safiyanu Yusuf, wanda tun da ya rasa aikin sa a kamfanin S.A.L shekaru hudu baya, har yau bai sake samun wani aiki ba.
Ba ‘yan adawa kadai ke sukar gwamnatin Muhammadu Buhari ba, da dama daga cikin wadanda suka sha wahala akan gwamnatin aka watsar da su na kan ra’ayin cewa idan ma mutum na kallon ba a tafka sata a karkashin wannan gwamnatin, to ya na yaudarar kan sa ne.
NI DA LAWAL KASUWAR WAMBAI
“Ai ga wadanda aka bai wa mukamai nan mu na ganin daga masu gina gidaje sai masu kara aure. Kuma kudaden da suke kashewa a wurin auren kadai, idan ka yi nazari sai ka ga ba su taba ko ganin kwatankwacin su ba, sai dai a hoto kawai.” Inji Lawal Bashir, wani dan kasuwa mai sayar da bulawus a Kasuwar Kofar Wambai, wanda ya gayyace ni daurin aure gidan sa, amma na kira shin a ba shi hakurin rashin halartar da ban yi ba, daga nan kuma mu ka goce hirar al’amarin kasa.
“Ni matsala ta da APC shi ne, duk kuskuren su, ba su karbar gyara. Amma kuma duk alherin gwamnatin baya to ba su yarda alheri ba ne. Yanzu dubi yadda gwamnatin Jonathan ta gina jami’o’i na tarayya har 13, kuma wasu gwamnatocin jihohi na PDP kamar Katsina, Kano, Jigawa, Gombe, Kaduna da sauran su duk suka kafa jami’o’i. Don Allah da a ce babu wadannan makarantu a yanzu, da me ka ke tsammani wajen yawan masu zaman-dirshan a gida a bangaren yaran mu masu gama jami’a? Inji Alhaji Abubakar Jibrin, wani telan da ke dumka kayan mata da na yara. Shi kuma biyo ni yay i har jikin mota mu na hirar matsalolin kasar nan tare da shi, a lokacin da na je wurin sa zan karbo dinkin yara.
MAI WANKIN MOTA YA HAU NI DA FADA
Wani magidanci mai wanke motoci a Na’ibawa mai suna Mohammed Ali. Ya hau ni da fada a lokacin da ya ke wanke min mota, a lokaci daya kuma mu na hirar duniya da shi: “Kai fa dan jarida ka zo ka tambaye ni ne don ka ji ina yabon Buhari ko? To ai ni yanzu na daina yin komai a duhu. Saboda dai na duba a Kano na ga ba mu iya siyasa ba. Kullum mu dai Buhari, Buhari, Buhari. To don Allah me ya yi mana?
“Mu ke nan kullum zagin Janar Babangida, amma duk wani abin kirki idan ka duba, in banda na zamanin audu Bako, to duk aikin gwamnatin tarayya ne a zamanin Babangida.”
“Buharin nan fa tun da ya hau mulki bai kara zuwa Kano a mota ba. Bai san yadda titin Zariya zuwa Kano ya lalace ba, kuma bai san yadda na Funtuwa zuwa Kano ya lalace ba. Sau daya ya zo Kano, shi ma sai da muka yi masa gori. Sauran zuwan biyu da ya yi kuwa duk daurin auren manya ne ya kawo shi, bai zo don abin da ya shafe mu ba. To don me zan yi ta bata lokaci na a kan sa?
Wani mai goyon bayan jam’iyyar PDP, mai suna Aliyu kuwa, ce min ya yi, ya yarda an yi barna a zamanin PDP. Amma da yawan wadanda suka yi barna a yanzu sun shige cikin APC, an daina ganin laifin su.
“Ina tabbatar muka duk ranar da muka kayar da APC, za ku rika jin tabargazar da za a rika fallasawa gwamnatin ta yi. Nan fa kiri-kiri a bainar jama’a Buhari ya ce Abacha ba barawo ba ne. Amma ga shi sai dawo wa gwamnati da kudaden da Abacha ya wawura ake yi. Kai ka san Buhari na da matsala.
“PDP dai aka raina, su kuma gwamnonin APC na yanzu da Buhari ya rika gabza wa kudade domin su biya albashi, da yawan su sun ki biya, amma ya zuba musu idanu. Kuma bai ce musu ku dawo da kudaden da na ba ku ba. Wai wannan mutumin ne zai dame mu da labarin abin da aka yi lokacin PDP. To shin a na sa lokacin kuma fa?”
A gaba na a ranar Lahadi, bayan an daura aure a wani kofar gida a Bachirawa, kusa da Ramin Tifa, kofar gidan Danlami Rawayau, Kano, gardamar siyasa ta rukume a kan sunayen wadanda ake zargin sun wawuri dukiya.
GARDAMA A WURIN DAURIN AURE
Wani Alhaji Mansir na hakikicewa ya na kare PDP. “Yanzu dai a kasar nan duk shedancin ka idan ka na APC, to kai waliyyi ne. Sun ki yarda Rotimi Ameachi ya yi barna a jihar Rivers, kuma ba su yarda tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi ya yi barna a jihar Ekiti ba. Shi ne ma Ministan Karafa a yanzu, kuma ya kusa ajiye mukamin minista ya sake neman takarar gwamnan. Amma da ya ke APC ba su son Saraki, shi kadai ne mabarnaci.
“Ai dama wannan halayya gado su ka yi wajen Buhari. Shi ne ya ce ya yi bincike Babachir Lawal bai ci kudin yi wa ciyawa fitiki ba, sai da majalisa ta tabbatar masa cewa kumbiya-kumbiya ya ke yi, sannan ya yi shiru.
Kada ku manta, Buhari ya taba cewa Audu Ogbe barawo ne, domin ya daure shi a lokacin da ya yi mulkin soja, aka yi masa daurin sama da shekaru 30. Babangida ne ya fito da shi. Amma yanzu Buhari ya nada shi ministan gona a gwamnatin sa.”