Mata masu ciki sun yi zanga-zangar tsawwala kudin haihuwa

0

Wasu mata sama da 100 masu ciki sun rufe bangaren yin awo na asibitin Akure dake jihar Ondo don nuna fushin su ga tsawwala kudin haihuwa da asibitin ke yi idan suka zo haihuwa.

Da zarar mace ta dauki ciki, hankalin ta zai fara tashi saboda irin kudin da za ta nema domin biya a asibiti. Idan mace za ta haihu, sai ta biya naira 25,000, idan kuma aiki za ayi mata sai ta biya naira 50,000, bayan kananan abubuwan da ake bukata za ta siya a asibitin gwamnati.

A dalilin haka matan sun yi kira ga gwamnan jihar Oluwarotimi Akeredolu da ya bincike wannan matsala musamman yadda ma’aikatan asibitin kan ce wai gwamnatin ne ke sa su karban wannan kudi daga hannun su.

Shugaban asibitin Moses Adewole a nashi tsokacin ya karyata yawan korafi na matan.

Moses ya ce Naira 9,500 ne kachal ake biya idan mace ta zo haihuwa a asibitocin gwamnati na jihar.

Share.

game da Author