Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya, Janar Tukur Buratai, ya rattaba hannun amincewa da karin girma na musamman ga zaratan sojojin Operation Lafiya Dole su 3,729 da a yanzu haka ke cikin Dajin Sambisa.
Wannan karin gira a ta bakin kakakin rundunar sojojin, Texas Chukwu, ya ce an yi shi ne saboda a nuna yabawa kan irin jan aiki da jajircewar zaratan sojojin a kan aikin su na kare kasa da ‘yan kasa da su ke gudanarwa.
Daga cikin wadanda aka kara wa girman, akwai Manyan Saje 223, wadanda aka maida Warrant Officers, sai kuma Saje su 511 da aka kara wa gurma zuwa Babban Saje.
An kara wa Kofur 994 girma zuwa Saje.
Sauran sun hada da Lance Corporals 1064 da aka kara wa mukami zuwa Kofur. Akwai kuma farabiti 932 da aka kara wa girma zuwa Lance Corporals.
Discussion about this post