Rundunar ‘yan sanda ta kori jami’in ta wanda ya kashe dan acaba saboda ya ki ba shi cin hancin naira 50.
Wannan al’amari dai ya faru ne a Abakaliki, babban birnin jhar Ebonyi. Haka kakakin ‘yan sanda ta jihar, Loveth Odah ta bayyana wa manema labarai jiya Laraba.
Ta ce wanda ya aikata laifin za kuma a gurfanar da shi a kotu ranar Juma’a da tuhumar kisan kai.
Dan sandan dai ya bindige dan acaba mai suna Ofim Ejike a kan titin Waterworks, cikin Abakaliki. Wanda ya yi harbin, mai suna Onyebuchi Nweke, Saje ne na ‘yan sanda, wanda ke aikin farautar ‘yan fashi da makami a jihar.
Tun da farko dai Gwamna Omahi ne na jihar Ebonyi ya bada umarnin cewa a tabbatar duk inda dan sandan ya shiga an kamo shi.