Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnati ta amincewa wa hukumar gudanar da binciken magunguna na kasa (NAPRED) da kamfanin sarrafa magunguna ‘May and Baker Plc’ da su fara sarrafawa da siyar da maganin cutar sikila mai suna ‘Niprisan’ a kasar nan.
Ya sanar da haka ne ranar Laraba bayan sun kammala taron kwamitin zartarwa na mako mako a afadar shugaban kasa.
Adewole yace gwamnati ta yi haka ne domin rage illar da cutar ke yi wa mutane a Afrika da sauran kasashen duniya.
Ya ce shekaru 20 da suka wuce hukumar NAPRED ta fara sarrafa wannan maganin wanda bayan an tabbatar da ingancin maganin hukumar ta durkushe saboda rashin kudi.
Adewole ya ce yanzu gwamanti na kokarin farfado da hukumar domin kawar da illar da cutar ke yi wa mutane a duniya.
” Bincike ya nuna cewa kashi 25 bisa 100 na mutane Najeriya na fama da wannan cutar sannan sama da miliyan biyu na dauke da kwayoyin cutar a jikin su.”
” Masu dauke da wannan cutar basu iya jure wa wahala na lokace mai tsawo.”
A karshe Adewole ya ce wannan dabarar da gwamnati ta dauka ya budo hanyoyin ci gaba a fannin kiwon lafiya a kasar nan.
” Gwamnati ta amince a bude fannin binciken magungunan gargajiya sannan za a gina babbar asibitin kula da mutanen da suka kamu da ciwon tabuwar hankali.”
Discussion about this post