Gwamnatin Kaduna ta maka shugaban mabiya Shi’a, Sheikh Ibarhim El-zakzaky kotu, ta na zargin sa da laifin kisa.
An maka El-zakzaky kotu ne a daidai lokacin da mabiyan sa ke ta kara tururuwa a Abuja, su na zanga-zangar tilas sai an saki jagoran na su.
Lauyan sa Femi Falana ya ce an aika masa da sammacen karar da aka kai shehin malamin tun a ranar 18 Ga Afrilu, 2018.
Idan ba a manta ba, tun cikin watan Disamba, 2016, kotun Najeriya ta bada umarnin a saki malamin, amma gwamnatin tarayya ta yi kunnen-uwar-shegu da umarnin wanda kotu ta bayar.
Wannan cajin kisa da aka yi wa malamin har caje-caje takwas, ya zo ne bayan shi kan sa malamin ya rasa ‘ya’yan sa har guda shida, wadanda sojoji suka bindige a wurin zanga-zanga a Zariya.
A lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan, an kashe masa yara biyu, lokacin mulkin Buhari kuma a waki’ar Buratai an kashe masa ‘ya’ya hudu.
A zaman yanzu kuma ya rasa ido daya, yayin da dayan kuma ana ta kokarin fita waje da shi domin a yi masa aiki, amma gwamnatin tarayya ta ki sakin sa.
Discussion about this post