Za a yi wa yara 350,000 allurar rigakafi a jihar Ondo

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Ondo Wahab Adegbenro ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta fara yi wa yara kanana allurar rigakafi a kananan hukumomi 18 na jihar.

Adebenro ya fadi haka ne ranar Litini inda ya bayyana cewa za su fara yiwa yara allurar ne a cibiyoyin kiwon lafiya 33 dake karamar hukumar Akoko ta kudu domin kawar da yawan mutuwan yara da jihar ke fama da shi.

Ya ce suna sa ran cewa za su yi allurar rigakafi cututtukan shawara, bakon dauro da ‘Vitamin A’ wa jarirai ‘yan watanni tara.

A karshe Adebenro ya ce gwamnati ta tanaji Naira miliyan 39 wanda za a yi amfani da shi wajen yi wa yara allurar rigakafin bakon dauro.

” Hakan zai taimaka mana wajen ceto rayukan ‘ya’yan mu daga cututtukan da ka iya kashe su.”

Share.

game da Author