Shugaban hukumar kula da Cibiyoyin Kiwon Lafiya a matakin farko (NPHCDA) Faisal Shuaib ya bayyana cewa a cikin shekaru 10 ma su zuwa Najeriya za ta bukaci Naira biliyan 824 don siyo maganin allurar rigakafi.
Ya fadi haka ne a taron ranar yin rigakafi na nahiyar Afrika ta shekara 2018 wanda ake yi duk shekara a watan Afrilu.
Faisal ya ce samun wannan kudade zai taimaka wajen yi wa yara kashi 84 bisa 100 allurar rigakafi.
” Adadin yawan yaran da basu yi allurar rigakafi ba a Najeriya ya kai miliyan 4.3.”
” Ya zama dole Najeriya ta samar da isassun kudade domin siyo maganin rigakafi da za ayi wa yara da ke kasar nan.
” A wannan shekara hukumar NPHCDA ta bukaci dala miliyan 93 don yi wa yara allurar rigakafi amma abin da gwamnati ta bada dala miliyan 33 ne suka samu.”
Daga karshe Faisal ya tabbatar da cewa hukumar su zata yi iya kokarinta wajen tabbatar da cewa duk yara dake kasar nan sun sami yin allurar rigakafi.
Discussion about this post