KOKUWAR ZAMA SHUGABAN APC: Oshimhole da Oyegun sun ja daga

0

Idan dai ba a man ta ba, zaben shugabannin jam’iyyar PDP da akayi gab da zaben 2015 ne ainihin makasudin samun rarrabuwa a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

Daya daga cikin abubuwan da jam’iyyar APC tayi ta gudu wa shine ruftawa irin wannan baraka da hakan yasa ta nemi ta daga zaben shugabannin jam’iyyar sai bayan an kammala zabukan 2019.

Yanzu dai an fara samun irin wannan baraka da tayi ta yi wa gudun famfalaki, domin kuwa shugaban jam’iyyar John Oyegun ya bayyana ra’ayin sa na tsayawa takarar kujerar shugabancin jam’iyyar a gangamin jam’iyyar da za a yi ranar 14 ga watan Mayu.

Wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar APC na yankin kudu Maso kudu sun karyata rahotannin da ya karade shafunan jaridun kasar nan cewa wai sun yanke shawarar mara wa tsohon gwamnan jihar Edo  Adams Oshimhole baya da shima ya fito takarar zama Shugaban jam’iyyar.

Sun ce ba haka bane duk da ko sun tabbatar da shi Adam din ya halarci taron jam’iyyar na yankin.

Shi dai Adam Oshimhole na da daurin gindin Jagorar jam’iyyar, Bola Tinubu da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Tun a baya dai ana takun saka ne tsakanin shugaban jam’iyyar da tsohon gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu inda a lokutta da dama sun yi ta samun sabani a tsakanin su.

Hakan dai ya fito fili karara ne tun a lokacin zaben dan takarar gwamnan Jihar Ondo sannan kuma da tsoma baki da yin katsalandan a aikin sasanta ‘ya’yan jam’iyyar da basa ga maciji a tsakanin su da Buhari ya nada Tinubu yayi.

Tuni dai Tinubu ya zargi Oyegun da neman watsa masa kasa a ido, yayi watsi da aikin.

Masu yin fashin baki a harkar siyasa suna ganin lallai canza Oyegun shine mafita ga jam’iyyar domin bashi da wani tasiri a jam’iyyar.

Kowa na Iya juya Shi sannan shi kan sa Shugaban kasa ya kasa gane in da alkiblar sa ta karkata zuwa.

Wasu da dama na ganin Oyegun ya zama karen farautar shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, sai yadda yayi da shi.

Hakanne wasu ke ganin idan dai APC na so ta Iya yin tasiri a dimbin kalubalen da ya dabaibayeta  dole ne fa ta fara tankade da rairaya tun daga gida.

Yanzu dai ga fili ga doki.

Share.

game da Author