Yadda mu ka kulla yarjejeniya da Boko Haram aka saki daliban #Dapchi – SSS

0

Shugaban Jami’an Tsaro na Sirri (SSS), Lawan Daura, ya bayyana wa Shugaba Muhammadu Buhari yadda hukumar sa ta kulla yarjejeniyar sako dalibai mata na makarantar sakandaren Dapchi da suka arce da su tun ranar 19 Ga Fabrairu, 2018.

Da ya ke jawabi da yammacin Juma’a, a lokacin da aka gabatar wa Shugaba Buhari dabiban, Daura ya ce sun dauki wannan mataki ne sakamakon umarnin da Buharin ya bayar cewa jami’an tsaro su bi hanyoyin duk da suka dace domin a ceto dukkan wadanda su ke tsare.

Ya ce daga nan su ka dukufa wajen tattauna hanyoyin neman maslaha ta karkashin kasa.

Daura ya kara da cewa sharuddan da Boko Haram suka bayar kawai su ne a tsagaita kai wa juna hare-hare,domin a ba su sararin daukar yaran a mota da kan su, su maida su har inda suka sato su.

Sun kuma ce su na so a tabbatar musu da cewa jami’an tsaro ba za su yi musu kwanton-bauna su rufar musu da hari ba bayan sun maida yaran.

“Ta yadda aka bi aka maido yaran abu ne mai matukar wahalar gaske. Saboda sai da aka rika yin la’akari da abubuwa da dama, kamar yadda za a yi jigilar yaran, hanyoyin da za a rika yin ratse da yanke wadanda ta nan ne za a bi a maida yaran, sannan kuma mun yi la’akari da cewa ba a wuri daya aka tsare yaran ba, sun rarraba su.

“Mun kuma yi la’akari da wuraren da shingayen jami’an sojoji su ke. To wadannan sun kara tsaurara matakan dawo da yaran.

Shugaban na SSS, ya kara da cewa baya ga batun da wo da yaran, an kuma fadada tattaunawar da nufin a samu tsagaita wuta da ajiye makamai na dindindin, domin a daina yakin.

Inda muka fi karfafa batutuwa su ne wajen makomar maharan da ake tsare da su, sai kuma ‘yan Najeriya wadanda Boko Haram su ke tsare da su, wadanda ba su ji ba, ba su gani ba. Sai kuma batun yin afuwa ga duk wani dan ta’addar da ya ajiye makamai, ya tuba.

Ya kara da cewa batun yarjejeniyar ya dan dagule daga farko sosai, kasancewa kawunan Boko Haram a rabe ya ke, kowane bangare ya ja ta sa runduna daban, kuma ya na da mafaka a wuraren da su ka yi kaka-gida su ke kai hare-haren sunkuru.

“Babbar matsalar soshiyal midiya a kan wani abu na sirri da ake son aiwatarwa da kuma kalaman subul-da-baka ko kasassabar jami’an gwamnati wadanda ba su cancanta su yi magana a kan wasu al’amurra ba, hakan ma sun haifar mana da kalubale yadda kusan har su ka kusa bata kokarin da mu ke yi”

HALIN DA YARAN KE CIKI

Daura ya kara da cewa bayan an saki yaran, an dauke su zuwa asibitin jami’an SSS, inda aka duba lafiyar su, da sauran kulawar da ta kamata.

An yi musu bincike, an samu masu gocewa a jikin su har yara hudu.

“Kusan gaba dayan su kowace ta na da cututtuka a jikin su, domin tun da aka dauke su, har tsawon wata daya babu wadda ta yi wanka.”

Ya ce kuma a lokacin da ake duba su, an tafi tare da shugabar makarantar da mataimakiyar ta, da kuma iyayen yaran.

MAFITA

Daga nan sai ya bada shawarar a ci gaba da tattauna yadda za a sako dukkan wadanda ke hannun Boko Haram a tsare. Ya kuma yi kira a kara samun hadin kai a tsakanin bangarorin jami’an tsaro. Sai kuma kiran da ya yi a kara tsaurara tsaro a makarantun sakandare, musamman na kwana.

Ya shaida wa Buhari cewa akwai karin wasu yara biyu da Boko Haram suka hado da su, suka Maida, wato Hafsat Haruna mai shekara 11, wata ‘yar firamare aji 6, sai Mala Maina, yaro dan shekara 13, shi ma dan aji shida na firamare.

Daura ya ce akwai wasu yara shida da ba a sako ba tukunna, amma ana ci gaba da tattaunawa a kan yadda za a sako su.

Share.

game da Author