Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yayi matukar mamakin yadda Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ya bijire wa umarnin da ya ba shi cewa ya koma Benuwai da zama har sai ya warware matsalar rikicin Fulani da makiyaya.
Ya ce gwamnatin sa ta damu kwarai da irin zubar da jinin da ake yi, sannan ya sake shan alwashin kawo karshen rikicin ba da dadewa ba.
A daidai lokacin da kasar nan ta rude dangane da kisan mutane 70 a jihar Benuwai ne Buhari ya ba Sufeto Janar Idris umarnin ya koma da zama jihar Benuwai har sai an shawo kan matsalar tukunna.
Sai dai kuma Idris ya je ko kwana daya bai yi ba, abin da ya jawo caccakar sa, a gefe daya kuma Buhari tun a lokacin bai yi masa komai ba.
Buhari, ya gana da Fulani da manoma da jami’an gwamnati da sauran al’umma a jihar, ya ce ba daidai ba ne, kuma ba gaskiya ba ne da ake cewa gwamnatin sa ba ta damu da rikicin da ke faruwa a jihar Benuwai ba.
Ya ce ba gaskiya ba ne. Bai yiwuwa a ce shi ko gwamnatin sa ba su damu da kashe-kashen da ake yi a jihar Benuwai ko sauran jihohi ba.
Ya ce za a kawo karshen matsalar domin gwamnatin sa a kullum da wannan matsala ta ke kwana ta ke tashi.
Daga nan sai ya ce bai taba sanin cewa Sufeto Janar Idris ko kwana daya bai taba yi a Benuwai ba. “Ban taba sanin haka ba, sai yau din nan da na ke ganawa da ku na ke jin labarin ko kwana daya bai taba yi ba.”
Sai dai kuma Buhari ya ce a inda suke taron ba wuri ne da ya dace a rika yamadidi da rashin cika-aikin wani jami’in gwamnati ba. Daga nan ya roke su da a ci gaba da zama lafiya da juna.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES ba ta san dalilin da ya sa Buhari ya ce bai san Idris ko kwana daya bai taba yi a Benuwai ba, domin a ranar 1 Ga Fabrairu, 2018, ta buga labarin “Yadda Sufeto Janar Ibrahim Idris ya bijiere wa umarnin Shugaban Kasa, ya ki komawa Benuwai.”