Za mu siya wa Uba Sani fom din takarar Sanata na Kaduna ta tsakiya – Kungiyar Matasa

0

Kungiyar matasa a Kaduna mai suna ‘Matasan Kaduna, wato ‘ Kaduna Youth’ ta bayyana wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa da zaran mai ba gwamnan Kaduna shawara kan harkar siyasa ya shirya sune zasu siya masa fom din takarar Sanata na Kaduna ta tsakiya a 2019.

Shugaban Kungiyar Umar Mohammed Magaji ya sanar mana haka bayan ganawa da suka yi da mambobin kungiyar a garin Fatika, dake karamar hukumar Giwa, Jihar Kaduna.

” Bamu san ko nawa bane za a siyar da fom din amma ka sani cewa tabbas Idan aka fara siyar wa zamu nemi ko bashi ne mu siya masa.

” Abin da ya sa kaga muke ta wannan hidima, mu ba siyasa bace kawai a gaban mu, mun ga mutum mai kishin matasa ne da talakawa, shine ya sa muka maida hankali domin ganin irin su ne ke wakiltar jama’a.

” Kwanan nan aka fadi irin miliyoyin da ake raba wa sanatoci. Ina tabbatar maka cewa Idan Uba ya tafi wannan majalisa, wallahi duk wata sai mutanen mazabar sa sun shaida.

A karshe Umar ya yabawa gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin gwamna Nasir El-Rufai kan kokarin gyara gari da yake ta yi musamman karkara.

” El-Rufai jarumi ne mai kishin talakawa, babu abin da za muce masa sai dai Allah ya maimaita mana.” Inji Umar.

Share.

game da Author