Amosanin ido da ake kira ‘Glaucoma’ cuta ce dake lalata jijiyoyin idanun mutum wanda idan ba a maida hankali ba yakan kai ga makanta.
Bayanai sun nuna cewa shi wannan cuta baya da wani hanya da zai baka alama ko ka kamu da shi, ballantana har kace bari ka nemi magani da wuri.
Wata likitan ido Fatima Kyari ta ce gano cutar da wuri ne kadai hanyar kauce wa makancewa domin cutar kan makantar da mutum farat daya ne, kuma akan sani ne idan ana ziyartar asibiti akai-akai.
Likita Fatima ta lissafo wasu abubuwa 10 domin wayar da kan mutane game da cutar kamar haka:
1. Yawaita zuwa asibiti domin yin gwajin ido ne kawai ake iya ganewa ko an kamu da cutar.
2. Amosani ido kan makantar da mutum farad daya.
3. Cutar kan dauki tsawon lokaci kafin mutum ya gane cewa ya kamu da ita sannan da zarar za ta bayyana sai kaga mutum baya gani nan take.
4. Ana gadon cutar daga iyaye da kakanni.
5. Idan har dai cutar ta kawo makanta ba a iya warkewa
6. Sama da 100,000 na mutane Najeriya na dauke da cutar ba tare da sun sani ba.
7. Cutar ta fi kama masu shekaru 40 zuwa sama.
8. Motsa jiki na taimakawa wajen kare mutum daga kamuwa da cutar.
9. Rashin shan taba an kare mutum daga kamuwa da cutar
10. Hawan jini na kawo cutar
11. Kare idanu daga hasken rana ta hanyar saka tabarau.
12. Yawaita cin abinci masu sinadarin ‘Vitamin A,C,E,D kamar su kwai, alaiyaho, madara, tumatir, kubewa,
ganyayyaki da adi sauran su.
13. Cin abincin dake dauke da sinadarin ‘Zinc’ kamar su naman kaza, naman sa, naman rago, naman talotalo.
14. Cin abinci dake dauke da sinadarin ‘Omega-3fatty acids’ kamar su, cin kwallon kashu, gyada, kifi, fiya da sauran su.