Majalisar Wakilai ta Tarayya ta bayyana cewa za ta rattaba hannu kan dokar kafa Dakarun Zaman Lafiya (Peace Corps Bill).
Makonni biyu da suka gabata ne Buhari ya ki amincewa ya sa wa kudirin hannu domin ya zama doka.
Majalisar ta ce tunda shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ki sa ka wa kudirin hannan, ita za tayi amfani da karfin iko da da dokar kasa ya bata ta sa wa kudirin hannu ya zama doka.
To sai dai kuma hakan ba zai yiwu ba, har sai idan Majalisar Dattawa ta amince da hukuncin da Majalisar Tarayya din zartas.
Wannan hukunci na kafewa kan rashin yarda da kin amincewar Buhari, an dauke shi ne a ranar Laraba, kamar yadda kakakin majalisar Hon. Abdulrazak Mamdas ya bayyana.
Ya shaida wa manema labarai a Majalisa cewa baya ga wannan kudirin, akwai ma wasu kudirori har guda 9 da majalisar za ta yi amfani da karfin ta su zama doka ba tare da amincewar shugaban kasa Buhari ba.
Wadannan kudirori kuwa sun hada da na Cibiyar Kula da Baitulmali, Hukumar Kula da Ayyukan Al’umma, gyaran dokar sauya launin kudi, kudirin dokar bai wa alkalai cikakkar damar kwace kudade ko kadarori da kuma kudirin dokar kafa tsarin kwangilar sayen kayayyakin hukumar ‘yan sanda.
Sauran kudirorin sun hada da na jami’an kiwon lafiya, kudirin cibiyar kula da basussuka da na jami’ar Wukari.
Sau da dama dai Majalisar Tarayya ta sha aika wa Buhari kudirori domin ya sa musu hannu su zama doka, amma ya na kin amincewa, ko kuma yayi biris da majalisa har sama da kwaaaki 30 da doka ta shar’anta cewa ya amsa bukatar amincewa ko a’a idan ba haka ba, majalisa kuma ta rattaba hannu akai ya zama doka.
Discussion about this post