A yau Laraba ne hukumar kula da ilimin Firamare na jihar Kaduna (SUBEB) ta fara horas da malamai makarantun Firamaren jihar 27,000 sanin makamashin aiki a fadin jihar.
Shugaban hukumar Nasiru Umar ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Kaduna inda ya kara da cewa malaman da za a horas sun hada da sabbin malamai 15,409 da aka dauka da kuma tsofafi 11,591 wanda dama ke karantar wa a makarantun jihar.
” Mun kebe kwanaki biyu domin horas da malaman sanin makamashin aiki a makarantu 254 dake kananan hukumomin jihar Kaduna.”
Umar ya ce gwamnatin ta yi haka ne domin samar wa malamai dabarun koyarwa don inganta su aikin su sannan bayan haka za a tura su makarntu domin ci gaba da koyar da daliban.