NOMAN SHINKAFA: Thailand ta karyata Audu Ogbe

0

Jakadan Thailand da ke Najeriya, Wattana Kunwongse ya karyata furucin da aka ruwaito kasar Thailand ta yi cewa wai ta zargi Najeriya da yin sanadiyyar durkushewar masana’antun casar shinkafar ta guda bakwai, saboda rage shigo da shinkafa da ake yi a nan Najeriya.

A cikin wata wasika da aika wa PREMIUM TIMES, jakadan ya ce kalaman Audu Ogbe sun karkatar da hankulan jama’a kuma sun baddala gaskiya, ya maye makwafin ta da karya.

Wattana ya kara da cewa tabbas ya yi magana da Augu Ogbe, amma ya karkatar da hakikanin maganar da suka yi su biyu.

Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya, ya ruwaito Audu Ogbe ya yi wannan kasassafa ce a wurin taron Kwamitin Rabon Takin Zamani na shugaban kasa, NAN da aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa.

A bakin Audu Ogbe, ya furta cewa, “ kamar makonni biyu da suka gabata, Jakadan Thailand a nan Najeriya, ya shigo har ofis na ya ce min mun kwance musu zani a kasuwa.

“Na tambaye shi wane laifi muka yi musu? Sai ya ce min kasar Thailand na da matsalar rashin aiki yi ga matasa.

Yanzu abin ya kara tsamari saboda mun rufe manyan masana’antun shinkafa guda bakwai, saboda Najeriya ke sayen kashi 95 bisa 100, amma yanzu ta daina saye.”

Sai dai kuma jakadan na Thailand ya ce karya Audu Ogbe ke yi masa.

Ya ce tabbas ya je ofishin sa kuma sun yi bayanai dangane da yadda kasashen biyu za su kara cin moriyar juna. Ya kuma yabi gwamnatin Najeriya.

Daga nan ya ce amma shi babu inda ya furta cewa harkar noman shinkafar Thailand ya gurgunce, domin ko a cikin 2017 sun fitar da shinkafar da aka saya daga kasashen waje, ciki har da Najeriya ta zunzurutun ton miliyan 11.48, kwatankwacin dala bilyan 5.1.

Sai ya nanata cewa tabbas Ogbe gwarzon mutum ne, kuma zai ci gaba da neman hadin kai ga ma’aikatar sa ta noma domin a kara kulla dankon zumuntar cin moriyar juna fiye da wadda ake yi tsakanin kasashen a yanzu.

Share.

game da Author