Babu dalilin saka sunan Buhari a titin Filato – Best

0

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Filato Shedrak Best ya bayyana cewa gwamnatin Lalong bata yi daidai ba saka wa titin Maraban Jama’a, sunan Buhari da tayi.

Best ya ce babu abin da Buhari ya to wa Jihar tun bayan zaben sa da akayi shekaru uku Kenan.

” Banga dalilin da zai sa gwamnati ta saka sunan Buhari a wannan Titi ba, ganin cewa in banda matsaloli da Jihar take fama da su da gwamnatin tarayya bata yi komai akai ba, babu abin da akayi.

Sai dai da yake hira ce akayi a gidan radiyon Jihar, tare da shi a wajen shirin akwai kwamishinan yada labarai Yakubu Datti.

Datti ya musanta wannan korafi na Best, inda ya ce ” Ko kudin tallafi na ‘Paris Club’ da Buhari ya ba gwamnatin Jihar abin yabo ne domin da ita ne gwamna Lalong ya biya lodin bashin albashin ma’aikatan Jihar ake bin gwamnatin Jonah Jang.”

Share.

game da Author