Yadda zan tika Buhari da kasa a 2019 – Mawallafin SAHARA REPORTERS, Sowere

0

A hira da babban Editan jaridar PREMIUM TIMES , Musikilu Mojeed yayi da Shugaban jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya bayyana cewa ya kammala shiri tsaf domin yin takarar shugabancin Najeriya a 2019.

A hirar Sowore ya fadi dabarun da zai bi ya tika Buhari da kasa, makomar kamfanin sa da sauran su.

” Idan ka duba sannan kayi nazari kan yadda Buhari ya gudanar da mulkin kasar nan zuwa yanzu, za kaga cewa babu wani abin arziki da aka tabuka. A ‘yan kwanakin nan aka sace daliban makaranta mata har guda 110 sabanin alkawarin samar da tsaro da yayi wa mutane a lokacin kamfen a 2015.

” Bayan haka kuma, maganan yaki da cin hanci da rashawa shima ya zama labarin gizo da koki. Babu wani abin azo a gani da aka tabuka.

Da aka tambaye shi ko a wace jam’iyya zai yi takara, Sowere ya ce har yanzu yana shawara tukunna.

” Ina shawara game da jam’iyyar da zan fito takara har yanzu tukunna. Yanzu dai ina kasar Amurka ina ta shiri sannan Ina ganawa da yan Najeriya dake zaune a kasashen waje, musamman Amurka.

Sowere ya kara da cewa Idan har ya zama shugaban Najeriya, zai kawo sauye-sauye da za su amfani ‘yan kasa da kasar baki daya.

” Za a inganta fannin kiwon Lafiyar kasar nan, Ilimi zai inganta, za a Samar was matasa ayyukan yi, sannan za mu gyara ayyukan gwamnati da na kasuwanci da dai sauran su.

Sannan ya kara da cewa siyasar sa ba ta siyan kuri’u bane ko shinkafa a raba wa mutane.

” Za mu canza salon siyasa a kasar nan. Ba siyasar siyan kuri’u bane za muyi ko na rabawa mutane shinkafa. Tsakanin mu da mutanen Najeriya ne za mu tara kudin da zamu yi aiki da shi a wajen kamfen.

Karanta Tattaunawar

PT: Me ya ja hankalin ka ka yanke shawarar shiga siyasa?

SOWORE: Ni dama ai na dade ina a sahun gaba wajen rajin nemen kawo ci gaba a Najeriya. Na farko tun ina dalibi na fara da kuma tasowa ta ina matsashi tun a lokacin mulkin sojoji mu ke gwagwarmaya. Tun cikin 1999, na ke gwagwarmayar kafa dimokradiyya da kuma tsaftace ta.

Amma a yanzu wani yunkuri ne mu ka yi, na dimbin ‘yan Najeriya wadanda aka yi watsi da su, aka wofintar da su. Wato wani sabon salon guguwar siyasa ne za mu karade kasar nan da shi.

PT: Ba za ka jingine rajin gwagwarmaya ba kenan?

SOWORE: Ai ita gwagwarmaya tafiya ce ta neman cimma kudirin da al’umma ke son ta cimma. Ai tun cikin 1999 mu ke a sahun gaba, amma mun kasa fitar da kasar nan daga surkukin matsaloli. Su wadanda mu ka tasa a gaba domin su ceci kasar sun kasa. Mu kuma sai muka yi kuskure mu ka koma gefe, muka zama masu sa-ido a kan zabe kawai da kuma shirya zanga-zanga.

A irin wanan matsaya da mu ke dauka, mun tafka kuskuren goyon bayan marasa tausayi da wadanda ba su san komai ba, sun zama shugabannin mu. To yanzu kuma sai na fahimci cewa ba za ka iya yin yasar rijiya ba, sai ka shiga cikin ta.

Obama da Mandela duk ‘yan gwagwarmaya ne, amma ba su yi nasara ba, sai da suka shiga ciki.

PT: Ka na so ka ce Buhari ya kasa kenan, kuma bai cancanci ya sake shugabancin kasar nan ba?

SOWORE: Ka dai ga yadda aka je aka sace dalibai mata a Dapchi, kwanan nan. Kiri-kiri Boko Haram suka loda sama da yara mata 100 suka tsere da su. A batun yaki da cin hanci kuma babu wani takamaimen hobbasa da ya yi guda daya. Boko Haram kuma na nan daram. Ga shi har yanzu sai funjum-funjum ya ke yi, ya kasa yin komai dangane da rikicin makiyaya da manoma. Abin sai ma kara muni ya ke yi.

PT: Ga shi zabe ya karato, saura kasa da shekara daya. Ka na can Amurka ne ko kuma? Yaushe za ka samu jam’iyar da za ka shiga kuma har ka tattara magoya baya?

SOWORE: Ai ina kan shirye-shiryen hada komai da komai. Ko daga nan inda nake, ina shirya neman goyon baya a cikin ‘yan Nijrriya mazauna kasashen waje. Watanni biyu da na je Najeriya kuma na dan zagaya an kuma yi taruka. Zan samu lokaci na zo na dade mu na tsare-tsare.

PT: Ka san fa siyasa a Najeriya sai da kudi. Ina za ka samu kudin yin wannan gagarimin shiri?

SOWORE: Kwarai kuwa na san da haka. Amma mu za mu bada karfi ne wajen nuna kishin neman mafita tare da taimakekeniya a tsakanin mu ‘yan Najeriya magoya baya. Sai kuma wadanda suka ji kan mu su ka bayar da gudummawa.

PT: Na ga dai kai dan kudancin Nijeriya ne, kuma jam’iyyu biyu manyacduk dan Arewa za su ba takarar shugaban kasa. Shin za ka jira ne sai 2023 ka fito takara ko kuwa?

SOWOERE: Wace tsiya tsarin karba-karba ya tsinana mana? Ni abin da na yi imani da shi, idan ana maganar ceto Najeriya, to duk maganar wata karba-karba duk a bar ta. Mu magoya bayan mu babu ruwan su da tsarin karba-karba, musamman da suka fahimci wanda ke jan ragamar kasar nan a yanxu ya shigo da bangaranci, kabilanci, fifitanci dac addinanci ya ragargaza hadin kan kasar nan.

Babu abin da karba-karba ya tsnana mana sai bada dama shugabannin su azurta kan su da kan su kawai.

PT: Amma fa kayar da Buahri zai yi maka whala fa. Ya za ka fafata da shi a 2019.

SOWORE: Na san ya na da magoya baya mana. Amma ai duk da magoya bayan bai yi nasara ba, har sai da ya jaraba sa’a sau uku, sai a karo na hudu ya yi nasara. Shi ma sai da aka yi gamin-gambizar jam’iyyu wuri daya sannan ya sha da kayar.

PT: Me za ka samar na ci gaba ga kasar nan idan ka zama sugaban kasa.

SOWORE: Najeriya ta shiga matsala saboda shugabannin baya ba su da tunanin tsara tafarki ko turba da lallai idan muka bai ta, to tabbas za mu kai gaci. Ka rabu da farffagandar da ka ke gani a NTA a na cewa tattalin arziki ya yi sama da sauran tasunniyoyi da ake yi mana. China ai sai da ta yi kyakkayawan tsari sannan ta kai inda ta ke yanzu a duniya. Sai ta yi amfani da yawan al’ummar ta ta gina kasar.

Amma mu yawan mu bai tsinana mana komai ba, sai kashe kasa da kashe tattalin ta. An sace kudade an an boye a wasu kasashe ana gna kasashen da kudaden mu. Dubi yadda aka samu ci gaba aka gina Dubai.

Maimakon mu kwaikwaye su, sai muka karkata wajen sace kudaden mu muna zuwa Dubai muna jibgewa.

PT: Ya za ka yi da Sahara Reporters kenan idan ka shiga harkar siyasa gadan-gadan ko kuma ka yi nasara?

SOWORE: Sahara Reporters za ta ci gaba da aikin tsage gaskiya da ta key i. Zan tsame hannu na kacokan na damka ta hannunn masu kishin da za su ci gaba da sa-ido kan gwamnati ko ma ta wace ce.

Domin a yanzu ta yi karfin da zan ce ba daga kaina ta fara ko ta tsaya ba. Akwai zarata sosai wadanda su ne ke tafiyar da ita a yanzu. Ba za ta kauce daga alkibla da turbar da ta ke a kai ba.

Share.

game da Author