An kashe Buharin Daji

0

Kasurgumin mai yin garkuwa da mutane, kuma shugaban barayin shanu a dajin Zamfara ya iske ajalin sa bayan wuta da ya sha daga jami’an tsaro na soji a wata artabu da akayi da shi a cikin wannan daji a makon da ya gabata.

Mataimakin gwamnan Jihar Zamfara Ibrahim Mohammed ya jinjina wa jami’an tsaro kan wannan nasara da suka samu.

Buharin Daji dai ya addabi mazauna kananan hukumomin Jihar Zamfara. A ‘yan kwanakin baya shine aka zarga da kai wa kauyen Birane, dake karamar Hukumar Zurmi hari, inda aka rasa rayuka da dama sannan aka sace wa makiyaya shanun su.

Share.

game da Author