A shirin zaben kananan hukumomi da za ayi a jihar Kano a karshen wannan mako, rundunar ‘yan san dan jihar ta sanar cewa za tayi amfani da jami’an ta 12,000 ne domin samar da tsaro ga mutanen jihar lokacin zabe da wuraren zabe.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Rabi’u Yusuf ya ce za suyi aiki ne tare da sauran jami’an tsaro da ya hada da jami’an NDLEA,FRSC,SSS da Civil Defence Corps.
Ya kuma kara da cewa sauran jami’an tsaron dake mallakin jihar ne kamar su Hisbah, KAROTA, Man’O’ War da ‘yan banga ba za su yi aikin samar da tsaro ba a wannan rana.
Bayan haka Yusuf ya ce gwamnati ta kafa dokar hana yin amfani da ababen hawa karfe 6 na safe zuwa 4 na yamma.
” Amma mutane za su iya fitowa don kada kuri’ar su ranar Asabar sannan za kuma mu hana duk wanda muka kama yana dauke da makami ta kowace iri ce yin zabe a wannan rana.”
Daga karshe Yusuf ya gargadi gidajen yada labarai kada su fadi sakamakon zabe sai hukumar Zabe ta jiha ta tabbatar da sakamakon.
Discussion about this post